Dan takarar shugabancin Najeriya a karkashin jam’iyyar APC mai mulkin kasar nan Bola Ahmad Tinubu ya ce ya fito ya yi ta maganganu a lokacin da ya ji a jikinsa cewa wasu mutane sun yi masa taron dangi sakamakon neman tikitin tsayawa takarar shugabancin kasar da yake yi.
Zancen Tinubu ya mamaye kafofin yada labaran Najeriya kwanaki gabanin zaben fid da dan takarar shugaban kasa, a lokacin da ya fito yana cewa shi ya fiddo shugaba Muhammadu Buhari daga murabus da ya yi a siyasar kasar, ya kuma yi ikirarin cewa shi ya dora Dapo Abiodun a kan kujerar gwamnan jihar Ogun, kana ya zabi Yemi Osinbajo a matsayin wanda zai zama mataimakin shugaban kasa.
Tinubu ya yi wannan ikirarin ne a gaban gwamnan jihar Ogun da kuma sauran wakilai da suka yi ta jinjina masa.
Da yake jawabi a yayin da ya kai ziyara fadar Oba na Lagos, Rilwan Akiolu a ranar Lahadi, dan takarar shugaban kasar ya ce har sai da aka kai lokacin da ya ji komai ya gundure shi.
Tinubu ya ce babu wani dan asalin jihar Legas da ya taba samun damar zama shugaban Najeriya, duk kuwa da gudummawar da jihar ta bayar wajen hadin kan kasar.
Tinubu ya samun galaba a kan a kan ‘yn takara 13 da suka fito neman jam’iyyar APC ta tsaida su takara shugabancin Najeriya a babban taron jam’iyyar da ya gudana a Abuja.
A wani labarin na daban kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyya mai mulkin Najeriya APC a zaben dake tafe a 2023, Asiwaju Bola Tinubu, ya ce ya mika sunan wanda ya zaba a matsayin mataimakinsa, ga hukumar zabe mai zaman kanta INEC.
Tsohon gwamnan na Legas ya bayyana haka ne a wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ba kuma tare da ya bayyana sunan da ya gabatar ba.
Kafin wannan lokaci dai Tinubu ya zabi Alhaji Kabir Ibrahim Masari daga jihar Katsina ne a matsayin wanda zai tsaya takarar mataimakinsa domin ya cika wa’adin da hukumar INEC ta kayyade.
Sai dai an tsayar da Masari takarar ne na wucin gadi ne har zuwa lokacin da za a kammala tuntubar juna tsakanin masu ruwa da tsaki na Jam’iyyar APC, kan wanda za a tabbatarwa takarar.