Tinubu na alhini kan mutuwar sojojin da jirginsu ya faɗo
Shugaba Bola Tinubu ya bayyana mutuwar wasu sojojin ƙasar da helikwaftansu ya faɗo a cikin jihar Neja, a matsayin ‘babbar asara mai tayar da hankali’ ga Najeriya.
A ranar Litinin ne wasu sojojin ƙasar suka mutu lokacin da jirgin da suke ciki ya faɗo a ƙauyen Chukuba kusa da ƙaramar hukumar Shiroro ta jihar Neja a tsakiyar Najeriya.
Tinubu ya ce sojojin na kan aikin hidimta wa ƙasarsu ne lokacin da suka gamu da ajalinsu.
Tun farko rahotanni sun ce jirgin na aikin kwashe sojojin da suka jikkata ne a fagen daga don kai su asibiti, lokacin da ya faɗo ƙasa, tare da kashe waɗanda ke cikinsa.
Wannan dai, shi ne karon farko da gwamnatin Najeriya ta fitar da sanarwa a kan mutuwar sojojin ƙasar da kafofin yaɗa labarai suka yi ta ba da rahotanni a jihar Neja.
Sanarwar Shugaba Tinubu dai, ta bayyana sojojin a matsayin “jajirtatu waɗanda ba su kula da hatsarin da za su shiga ba, a ƙoƙarin kare ƙasarsu da tabbatar da ganin al’ummominsu sun samu zaman lafiya”.
“Yayin da muke alhinin mutuwarsu, za mu ci gaba da tuna gudunmawarsu, ba wai a matsayinsu na sojoji kawai ba, har ma da kasancewarsu gwaraza waɗanda suka sadaukar da rayuwarsu domin samun zaman lafiya da tsaron ƙasarmu”, in ji Tinubu.
Shugaban ƙasar ya ce “mun yaba da sadaukarwa da jajircewar da suka yi wajen kare ƙasarmu”.
“A madadin ƙasarmu, ina miƙa saƙon ta’aziyya ga iyalan sojojin, da babban hafsan tsaron ƙasa, da babban hafsan sojin sama da babban hafsan sojin ƙasa, da babban hafsan sojin ruwa, da kuma illahirin rundunar sojin Najeriya”, in ji shugaban ƙasar.
Rundunar sojin saman Najeriya ta fitar da wata sanarwa ranar Litinin tana tabbatar da faɗuwar jirgin helikwaftan ƙirar MI-171, wanda ta ce ya je ne don kwashe waɗanda suka rasu ko kuma suka jikkata.
A cewarta, jirgin ya faɗo ne da misalin ƙarfe 1 na rana bayan ya tashi daga Makarantar Firamaren Zungeru a kan hanyarsa ta zuwa Kaduna.
Kwanton-ɓauna ga sojoji kafin faɗuwar jirgi
A ƙarshen mako ne rahotonni suka ce ‘yan bindiga sun yi wa wasu sojojin Najeriya kwanton-ɓauna, tare da kashe wasu, da kuma raunata ƙarin dakaru.
Tun da farko, an kai sojojin ne don kawar da yawan sace mutane da kai hare-haren da ‘yan fashin daji ke yi kan ƙauyuka a ƙananan hukumomin Rafi da Wushishi da kuma Lavu duk a jihar ta Neja.
Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambato wata majiya daga sojin Najeriya na cewa sojoji aƙalla 26 ne suka mutu a kwanton-ɓaunar da ‘yan bindigar suka yi musu cikin daren Lahadi, tare da raunata ƙarin takwas.
Helikwaftan ya kwaso waɗanda suka jikkata ne domin kai su asibitin soji da ke jihar Kaduna mai maƙwabtaka a lokacin da ya rikito.
Kawo yanzu dai ba a san adadin mutanen da suka mutu sanadin faɗuwar jirgin ba.
Rundunar sojin sama a cikin sanarwarta, ta ce baya ga ma’aikatan cikinsa, jirgin ya kuma kwaso sojojin da aka kashe ko aka jikkata.
Haka zalika, AFP ya ambato majiyar da ke tabbatar da cewa helikwaftan na ɗauke da gawawwakin soja 11 da ƙarin soja bakwai da aka jikkata.
To sai dai wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, ya nuna wasu ‘yan fashin daji a wajen wani tarkace mai kama da jirgin da ya faɗo inda suke iƙirarin cewa helikwaftan ne kuma su suka harbo shi.
Cikin bidiyon na tsawon minti biyu da daƙiƙa 17, ana iya ganin ‘yan bindigar riƙe da miyagun makamai, suna iƙirarin cewa su yaran Dogo Giɗe ne – wani ƙasurgumin ɗan fashin daji da ya addabi sassan jihohin Neja da Zamfara da Kebbi.
A cikin bidiyon an kuma ga gawawwakin wasu mutane sanye da kaki irin na soja, yashe a wurin tarkacen jirgin, inda ‘yan bindigar suka yi iƙirarin cewa sojojin da ke cikin helikwaftan ne.
Shi ma Shugaban ƙaramar hukumar Shiroro, Akilu Isyaku Kuta, ya faɗa wa BBC Hausa cewa ‘yan fashin daji ne suka harbo jirgin da ke kan hanyarsa ta zuwa jihar Kaduna.
“Abin da muka sani shi ne, jirgin ya je wucewa ne ta daidai inda ɓarayin suka ya da zango, ba yaƙi ya je yi ba, wucewa zai yi zuwa Kaduna,” in ji Akilu.
Ƙananan hukumomin Shiroro da Wushishi na da nisan kilomita 75 daga Minna babban birnin jihar Neja.
‘Yan fashin daji sun daɗe suna tafka ta’asa inda suke da sansanoni a dazukan da suka ratsa jihohin Neja da Zamfara da Katsina da Kaduna, dukkansu a arewacin Najeriya.
Masana harkokin tsaro na cewa har yanzu akwai wurare masu faɗi da babu jami’an tsaron Najeriya a wurin, abin da ya sa ‘yan bindigar ke iko da su har ma suke saka wa mazauna yankunan haraji.
A watannin baya-bayan nan, yankunan arewa maso yammaci da tsakiyar Najeriya na yawan uskantar hare-haren ‘yan bindiga, wadanda ke kai samame ƙauyuka inda suka kashe mutane tare da sace wasu domin neman kuɗi fansa.