An nada Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje sarautar Aare Fiwajoye na kasar Ibadan, Ita kuma matarsa Farfesa Hafsat Ganduje an mata nadin sarautar Aare Fiwajoye na kasar ta Ibadan Manyan mutane a Najeriya sun hallarci taron nadin saurautar ciki har da dan takarar jam’iyyar APC a zaben 2023, Bola Ahmed Tinubu.
A yau Asabar 18 ga watan Yuni ne aka nada gwamnan Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje da matarsa Farfesa Haftsat Ganduje sarauta a masarautar Ibadan.
Mai martaba Olubadan na Ibadan, Dr Lekan Balogun ya nada Ganduje sarautar Aare Fiwajoye ita kuma Hafsat aka nada ta sarautar Aare Fiwajoye, rahoton Leadership.
Wasu manyan mutane a Najeriya sun samu halartar nadin sarautar cikinsu har da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APC a zaben 2022 kuma jagoran jam’iyyar na kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu.
A wani labarin na daban hukumar yakar cin da rashawa ta Najeriya EFCC, ta kafa wata tawaga ta musamman, wadda zata binciki gwamnan jihar Ekiti Ayodele Fayose a mako mai kamawa, kan zargin aikta laifin almundahana, kamar yadda jaridar Punch da ake wallafawa a kasar ta rawaito.
Hukumar Fayose, wanda ya kasance gwamnan jihar Eikiti tun daga ranar 16 ga Oktoba, 2014, zai rasa rigarsa ta kariya daga tuhuma a mako mai zuwa, ranar 16 ga watan Oktoban na 2018, lamarin da zai baiwa EFCC damar bincikarsa, tsarewa da kuma gurfanar da shi a gaban kotu kamar yadda dokokin Najeriya suka tanada.
EFCC na sa ran Fayose zai kai kansa ga hedikwatar ta dake Abuja, domin amsa tambayoyi kan zarge-zargen da ake masa.
Hukumar yakar cin hanci da rashawar na zargin Fayose da karbar naira biliyan 1 da miliyan 200 daga Sambo Dasuki, tsohon mai baiwa tsohuwar gwamnatin shugaba Jonathan shawara kan sha’anin tsaro.
A waccan lokacin dai an rawaito cewa Fayose ya yi amfani da kudin ne, wajen yakin neman zaben kujerar gwamnan jihar Ekiti, wanda ya lashe.