Hukumar NCC, ta ja hankalin masu mu’amala da shafin ko manhajar tik-tok sabida wani hange da hukumar tayi.
Gasa dai wacce aka fi sani da “Challenge” ba bakon abu bane ga yan Nigeria ko kuma masu amfani da kafar sadarwar zamani .
Kafar Tik-Tok ko kuma manhajar Tik-Tok kafa ce da ake wallafa hoto mai motsishiga sabuwar gasar Tik-Tok mai suna “Invisible Challenge” “Vedio” wanda tsawonsa bai wuce dakika 30.
Hukumar Sadarwa ta Najeriya ta gargadi ‘yan Najeriya kan hadarin tana mai cewa hakan kan iya sawa wayoyinka bairos.
Tace wannan gasar na baiwa wasu damar shigar da bairos din cikin na’o’urorin da kuke amfani da ita, inda su ringa sa ma bairso din daga kwamfuwutar su inji NCC.
NCC tace wanda suka kirkiri gasar suna amfani da wani bairos ne mai satar bayanai da ake kira WASP (ko W4SP) . kamar yadda jaridar Premium Times ta wallafa a rahotan ta.
“Ƙalubalen da mutane basu sani ba game da wannan bairos din shine, yadda wanda suka fito da wannan gasar zasu samu bayaninka kai tsaye ba tsare da wata kariya ba.
Sunayin hakan ne ta hanyar dora bidiyon gasar akan Tik-Tok tare manhajar (software) wadda ke dauke da bairos din.” in ji hukumar.
“Wadanda suka shiga cikin bidiyon tare da kwafarsa dan yi, to zasu zama na gaba-gaba da wannan bairos din “WASP” zai yi tasiri akansu sosai.
Zuwa yanzu an dakatar mutane miliyan guda bayan da aka fara yada bidiyon wanda ke dauke da wannan bairos din,” in ji hukumar.
Yadda Zaku Kare Kanku Hukumar ta NCC ta ce wasu hanyoyin da za a bi wajen dakile irin wadannan hare-hare sun hada da guje wa danna likau (link) din da basu da sahihanci ko amfani da manhajojin da basu da kariya.
Hakanan, duba manhajar da kake amfani da ita tare da cire wasu bayanai da suke da alaka da na’urarka ko kuma masu ajiye kalmar sirrin da akake amfani da ita.
Sannan ka inganta ma’ballan sirrin ka (password).