Tropical General Investments (TGI) Group ta kulla alaka da jami’ar Ahmadu Bello Unibersity (ABU), Zaria, domin bunkasa harkokin bincike da kere-kere hadi da sauran bangarorin ilimi daban-daban domin ci gaba mai ma’ana.
Hadin guiwar wacce ta samu asali yayin rattaba hannun yarjejeniyar fahimtar juna (MoU) da zimmar kyautatawa da inganta lamuran da suka shafi kirkire-kirkire a tsakanin masana’antar da kuma makarantar.
Yarjejeniyar fahimtar junan ta hada da sashi 18 da tsangayu 100 na jami’ar ABU, a yayin sanya hannun shugaban tsare-tsare na TGI, Habiba Suleiman, ta bayyana muhimman alfanun da hakan zai jawo wajen shawo kan matsalolin da ake samu a bangaren bincike da samun bayanai tare da nemo hanyoyin mafita.
Suleiman ta ce, “Mun bibiyi harkokin bincike da dama a jami’o’in kasar nan, amma ba a amfani da su yadda ya kamata. Wannan na daga cikin asarar da duniya take yi a yau, inda samun bayanai ya zama tamkar sarki.
Don haka da wannan hadin guiwar za a samu shawo kan muhimman matsaloli a wannan bangaren ta yadda za a assasa wani ginshiki na cigaba.”
A cewarta TGI Group ta himmatu wajen zuba hannun jari a ayyuka daban-daban ta yadda bangarorin masu ruwa da tsaki daban-daan za su shigo a dama da su da suka hada da jama’a, kamfanuni masu zaman kansu, masu zuba hannun jari na kasa da kasa, gami da masu kananan sana’o’i sama da 200,000.
Mukaddashin shugaban jami’ar ABU, Prof Kabir Bala, ya nuna gayar farin cikinsa kan wannan hadin guiwar da cewa hakan zai taimaka sosai wajen kara wa jami’ar azama a bangarenta na horas da kwararrun dalibai da nemo cigaba ga kasa.
Source: LEADERSHIPHAUSA