Tawagar ma’aikatan jiyya ta kasar Sin dake kasar Togo, ta yi aikin jinya kyauta a birnin Kara na lardin Kozah dake arewacin kasar.
Birnin Kara dake arewacin kasar, wanda kuma ke fama da koma baya a fannin kiwon lafiya, na da nisan kilomita 400 daga birnin Lome, fadar mulkiin kasar.
Tawagar ta baiwa marasa lafiya fiye da 6000 jiyya a wata cibiyar kiwon lafiya dake wurin, tare da baiwa cibiyar wasu kayayyakin kiwon lafiya.
Aikin da mambobin tawagar suka yi na samun karbuwa da yabo daga al’ummar wurin.
A cewar wani Jami’in cibiyar, tawagar kasar Sin ta baiwa jama’ar wurin tallafi bisa kwarewarsu a fannin jiyya, matakin da zai taimaka wurin ingantan kiwon lafiya.
Kana kayayyakin da tawagar ta bayar, za su kyautata halin da ake ciki a wannan cibiya.
Wannan tawaga dake kunshe da likitoci 14 daga lardin Shanxi na kasar Sin, ta bayyana cewa, yayin da ake cika shekaru 60 da Sin ta fara tallafawa nahiyar Afrika a fannin kiwon lafiya a bana, za su kara yada ruhin tawagar wato magance wahalhalu da ba da tallafi bisa iyakacin kokarinsu, tare da gudanar da ayyukan jiyya bisa gaskiya don amfanawa al’ummun Afirka. (Amina Xu)
Ofishin yada labarai na jihar Xinjiang mai cin gashin kanta, ya kira wani taron manema labarai a yau Litinin, inda ya bayyana cewa, a shekarar 2022, yawan kudin shiga da ko wanne mutum da ya fito daga kangin talauci a Xinjiang ya samu, ya kai RMB Yuan 14,951, wanda ya karu da Yuan 1608 bisa na shekarar 2021.
Kuma alkaluman sun zarce yawan matsakaicin kudin shiga da daidaikun mutumin da ya fito daga kangin talauci a kasar ke samu da yuan 609, wanda ya karu da kashi 12.1 bisa na makamancin lokacin a 2021.
Ban da wannan kuma, yawan karuwar ya zarce ta manoman kauyukan jihar da kashi 5.8%. (Amina Xu).
Source:LeadershipHausa