A kano dake arewacin najeriya, al’umma kamar yadda ake gudanarwa a duk garuruwan duniya sun gudanar da taron tunawa da ranar arba’in ta shahadar Imam Hussain (S.a), jikan manzon rahama (S.a.w.w), kuma taron ya kayatar matuka da gaske.
A wajen taron sanannen nmalamin addinin nan sayyid khidir lawan ne ya gabatar da jawabi inda ya tabo batutuwa da dama da suka shafi wannan rana ta arba’in din tare da bayyana darussan da za’a iya dauka dangane da wannan ranar da arba’in.
Kamar yadda majiyar mu ta tabbatar mana bayan musulmi mabiya matafiyar shi’anci, ‘yan uwa mabiya matafiyar ahlussunnah ma sun samu halartar wannan taro hakanan kiristoci ma sun samu halartar taron.
A kalla mutane dari uku ne suka samu halartar taron wanda ya gudana a babban birnin na kano.
An soma taron ne da karfe uku na yamma inda aka kammala karfe bakwai na yammaci, mabiya matafiyar iyalana gidan annabta dai wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a sun saba shiryawa gami da gudanar da ire iren wadannan taruka a duk shekara a garuruwa daban daban na najeriya domin tunawa da ranar arba’in din shahadar Imam Hussain (S.a) wanda jikan manzon Allah (S.a.w.w) ne.
An dai kashe Imam Hussain (S.a) ne shekara ta 61 bayan hijira a dajin karbala wanda yanzu babban birini ne a kasar Iraki, kuma tun daga wannan lokaci ake raya ranakun shahhadar sa har ma da ranar daya cika kwana arba’in da yain shahada.
A najeriya sakamakon isar hasken mazhabar iyalan gidan annabta musamman ta hannun babban shehin malamin nan sheikh Ibrahaim yaqoob Alzakzaky, al’ummar najeriya sun cigaba da raya wadannan ranaku kuma sauran bangarorin fahimtoci na addinai da akidu kanyi musharaka a wadanan taruka.
Bayan taruka a najeriya din dai a kan gabatar da jerin gwanon lumana a garuruwa da dama domin isar da sakon zaluncin da aka yima Imam Hussain ga al’ummomin kasar dama duniya baki daya.