Bayanan kudin da aka ware don tafiye-tafiyen shugaban kasa Muhammadu Buhari da mataimakinsa, Yemi Osinbajo sun fito a wani salon cin taliyar karshe da shugabannin zasuyi.
Hakazalika, kudin da shugabannin na Najeriya za su kashe a fannin abinci da goge wuya shi ma ya fito fili Kasafin kudin 2023 mai zuwa na nuni da cewa, ofishin Buhari da mataimakinsa kadai za su kashe N11.92bn a fannin tafiye-tafiye da cin abinci.
Bincike ya nuna cewa, kasafin kudin 2023 da shugaban kasan Najeriya Muhammadu Buhari ya gabatar a makon jiya ya bayyana adadin kudaden da ofishinsa da na mataimakinsa za su ci a fannin tafiya da abinci kadai ya zarce N11.92bn a shekarar.
Tafiye-tafiyen da ake nufi anan na cikin gida ne da wajen kasa, kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Jaridar Punch a yau Lahadi 9 ga watan Oktoba ta bayyana cewa, an ware N1.58bn domin kula da lafiyar jiragen sama, yayin da aka ware N1.60bn domin gyara injunan jiragen Gulfstream GV da CL605.
A bangaren majalisun kasa, an ware N100bn domin ayyukan mazabu, kamar yadda ya zo a kasafin da Buhari ya gabatar.
Fashin baki Legit.ng Hausa ta tattaro cewa, fashin bakin kasafin kudin ya nuna cewa, an ware N2.49bn ga shugaban kasa kadai domin zirga-zirga a ciki da wajen kasar nan.
Mataimakin sa kuwa, zai kone akalla N846.61m duk dai a zirga-zirgar da zai yi zuwa wasu kasashen waje da ma cikin gida Najeriya duk a salon na cin taliyar karshe.
Kudin man jiragen da za a yi zirga-zirga dasu kadai ya kai N250m, siyan kayayyakin kula da kuma kariya ga jiragen kuwa zai ci kusan N1.50bn yayin da za a kashe N650m ga sabon filin jirgin sama mai saukar ungulun tafi da gidanka.
Bugu da karin taliyar karshen, N36.15m za su gangara ne a matsayin kudaden da bankuna za su ja a matsayin kudin cajin hada-hadar cirewa da tura kudin kasafin na fannin jirage.
A bangare guda, jirage 10 da su Buhari ke hawa za su ci akalla N180m da sunan inshora.
Jiragen goma sun hada da: Boeing Business Jet (Boeing 737-800 ko kuma a ce NAF 001) Gulfstream 550 guda 1 Gulfstream V (Gulfstream 500) guda 1 Falcons 7X guda biyu Hawker Siddeley 4000 guda 1 AgustaWestland AW 139 guda biyu AgustaWestland AW 101 guda biyu Kasafin kudin abincin Buhari da Osinbajo Kamar yadda yazo a kasafin kudin, kayayyakin abinci da goge wuya na shugaban kasa da mataimakinsa zai ci akalla N508.71m.
Shugaba Buhari zai ci abincin N331.79m yayin da mataimakinsa Osinbajo zai ci N176.92m.
Idan aka yi duba cikin tsanaki, akwai karin zunzurutun kudi N750m daga kasafin kudin da Buhari ya gabatar a bara.
A wani labarin, gwamna Bala Mohammed na jihar Bauchi ya siffanta tsohon shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan da shugaba mafi nagarta da Najeriya ta taba yi.
Gwamnan ya bayyana hakan ne yayin da Jonathan ya ziyarce shi a Bauchi don yi masa ta’aziyyar rasuwar dan uwansa, kamar yadda Punch ta ruwaito.
A cewarsa: “Kai ne dai abu mafi kyau da ya taba faruwa a kasar da ake kira Najeriya.
Aikinka tukuru da sadaukarwarka ne suka sa Najeriya ta girma fiye da yadda ka same ta.
Source:legithausang