Hukumar INEC ta wallafa bayanai a game da takardun masu neman takarar shugabancin kasar Najeriya a 2023.
Atiku Abubakar da Bola Tinubu ake ganin su ne ‘yan gaba-gaba a zaben da za ayi a shekarar badi Kowanensu ya gabatarwa Hukumar INEC mai zaman kan ta bayanin takardun karatu da aikin da ya yi.
Premium Times ta ce ana ta surutu bayan ganin takardun ‘yan takarar shugaban Najeriya. Daga cikin wanda ya jawo magana shi ne Bola Tinubu.
Mutane su na mamakin yadda ‘dan takaran na APC ya yi gum a game da makarantun firamare da sakandarensa, yana mai ikirarin takardun sa sun bace.
An rahoto Bola Tinubu yana cewa tsakanin 1994 da 1998 ya bar Najeriya, da ya dawo kasar sai ya iske wasu boyayyen mutane sun dauke masa takardun sa.
A cewar Tinubu, ya yi digiri a bangaren ilmin kasuwanci da gudanar da mulki a jami’ar Chicago State University da ke kasar Amurka, ya kammala a 1979.
A Nuwamban 1982 ne tsohon gwamnan ya shaidawa INEC cewa ya yi hidimar kasa watau NYSC a Najeriya.
A game da sana’a, sai ya ce shi ‘dan siyasa ne. Alamar tambaya a game da WASC din Atiku Jaridar ta fahimci shi ma ‘dan takaran jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar bai yi cikakken bayani a kan jarrabawar WASC da yake ikirarin ya rubuta a 1965 ba.
A lokacin yana amfani da sunan Siddiq Abubakar, sai dai ‘dan siyasan mai shekara 75 ya nuna yana da digirgir a ilmin huldar kasashe daga jami’ar Birtaniya.
Bayan haka, Atiku bai fadawa INEC ya halarci makarantar firamare ta Jada, a jihar Adamawa ba. ‘Dan takaran ya yi bayanin cewa ya yi aikin kwastam a 1970s.
Shi ma abokin takarar Atiku a PDP wanda Likita ne, Ifeanyi Okowa bai yi bayanin makarantar firamaren da ya halarta a takardun da ya gabatarwa INEC ba.
Kwankwaso da Peter Obi Legit.ng Hausa ta fahimci Rabiu Kwankwaso ya nuna ya gama firamare a 1968 da sakandarensa a 1975.
Baya ga haka, yana da Diflomomin ND, HND da PGD. Har ila yau, ‘dan takaran na NNPP yana da digirin M. Sc da Ph.D da ya kammala kwanan nan. Kwankwaso ya gabatar da kundin digirinsa na PhD da ya yi. A karshe akwai Peter Obi wanda ya yi firamare zuwa jami’a tsakanin 1973 da 1984.
Obi mai shekara 61 ya yi aiki a banki, amma bai fadi zuwa yaushe ba. Kwankwaso ya ce ya yi aiki a matsayin Injiniyan ruwa na shekara da shekaru a Kano kafin shiga siyasa. Obi kuwa ‘dan kasuwa ne bayan zamansa ‘dan siyasa.