Tawagar Super Eagles ta Nijeriya ta samu tikitin shiga gasar cin kofin Afrika na 2023 (AFCON) bayan lallasa kasar Saliyo da Ci 3-2.
Zakarun Afirka sun samu tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar ne bayan da suka doke Saliyo da ci 3-2 a filin wasa na Samuel Kanyon Doe da ke Monrovia na kasar Laberiya a yammacin Lahadi.
Kelechi Iheanacho ne ya zura kwallo mafi muhimmanci a wasan da Super Eagles ta yi inda ya ci kwallo a mintin karshe 90+5 bayan fama da kunnen doki.
Victor Osimhen ne ya zura kwallaye Biyu a ragar Saliyo tun a mintuna 19 da 32 a zagayen farko.
A wani labarin na daban an bude kasuwar saye da sayar da ‘yan kwallo a Ingila daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin shekara ta 2023 zuwa 1 ga watan Satumbar 2023 kamar yadda aka saba yi duk shekara.
Kungiya za ta iya sayen dan wasan da bashi da yarjejeniya da wata kungiya, haka kuma za’a iya daukar aron dan wasa bisa kan doka da kulla kwantiragi bisa tsarin hukumar kwallon kafa ta duniya.
Haka kuma kungiya za ta iya daukar aron mai tsaron raga da zarar ba wani babban mai tsaron da yake da lafiya a kasa haka kuma za’a iya ciniki tsakanin kungiyoyin Premier League da ta EFL.
Kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a Ingila ta fara hada-hada daga ranar Laraba 14 ga watan Yunin 2023 zuwa 1 ga watan Satumbar 2023 kuma za’a iya kara wa’adi a karshen ranar rufe kasuwar idan an kusa kammala wani cinikin ko daukar aron dan wasa, amma lokaci bai ba da ikon cimma matsaya ba.
A Faransa kuma tun daga ranar 19 ga watan Yuni kasuwar ‘yan kwallo za ta fara ci a gasar Ligue 1 da sauran wasannin, wadda za ta karkare ranar 1 ga watan Satumbar 2023.
Sannan a kasashen Sipaniya da Jamus da Italiya kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a La Liga da Bundesliga da kuma Serie A za ta fara ci daga ranar 1 ga watan Yuli haka kuma za’a karkare hada-hada ranar 1 ga watan Satumbar 2023.
A kasar Amurka kuwa tuni aka ci kasuwar kwallon kafar Amurka daga 31 ga watan Janairun 2023 zuwa 24 ga watan Afirilun 2023 sannan za’a sake bude kasuwar daga 5 ga watan Yuli zuwa 2 ga watan Agustan 2023.
Ana fara kakar kwallon kafar Amurka daga 25 ga watan Fabrairu, wadda za ta rufe ranar 21 ga watan Oktoban 2023 wanda hakan yake nufin ba tare ake tafiya tsakanin Amurka da nahiyar turai ba.
Can kuwa a kasashen Argentina da Brazil tuni aka ci kasuwar cinikayyar ‘yan kwallo a Brazil, ana sa ran za’a sake yin hada-hada daga 14 ga watan Yuli zuwa 13 ga watan Agustan 2023.
An rufe kasuwar ranar 2 ga watan Fabrairun 2023, sai dai ba a bayyana ranar da za’a sake bude ta ba, amma ana sa ran sake cinikayya a cikin Yunin 2023 kamar yadda aka saba.
A Australia ma kasuwar cinikin ‘yan kwallo a Australia ta ci daga cikin Oktoba zuwa Mayu sannan za kuma a sake bude kasuwar daga 24 ga watan Yulin 2023 zuwa 15 ga watan Oktoban 2023.