Sudan Kungiyar IGAD Zata Shiga Tsakanin A Rikicin Siyasar Kasar.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen gabacin Afirka IGAD ta yanke shawarar nada manzo na musamman zuwa kasar Sudan don shiga tsakanin sojoji masu mulki da kuma ‘yan siyasa wanda suka daage sai sojojin sun sauka sun mika mulki ga fararen hula.
Jaridar Sudan Tribun ta bayyana cewa kungiyar ta yanke wannan shawarar ne bayan da kwamitin gano gaskiyan abinda yake faruwa a kasar Sudan ya dawo mata da cikekken rahoton yadda rikicin siyasar kasar Sudan take.
Kwamitin binciken ya je kasar Sudan ne a ranar 29 ga watan Jenerun da ya gabata sannan ya mika rahotonsa ga kungiyar a ranar daya ga watan Fabrairu da muke ciki.
Labarin ya nakalto babban sakataren kungiyar Workneh Gebeyehu yana cewa a cikin watan Maris mai zuwa ne shuwagabannin kasashen kungiyar na IGAD zasu nada jakada na musamman a kasar Sudan a taron da zasu gudanar a birnin Kampala na kasar Uganda.
A lokacin Ziyarar dai Workneh Gebeyehu wanda ya jagoranci yawagar IGAD zuwa Sudan, bayan ganawa da sojoji masu mulkin kasar Sudan ya gana da shuwagabanni manya-manyan jam’iyyun siyasar kasar wadanda suka hada da Jam’iyyar ‘National Ummah Party’, ‘The National Charter’, kungiyoyin Darfur, da kuma ‘National Libration party’ har’ila yau da kuma Sudanese Communist Party. Kasar Sudan dai ta fadi cikin rikicin siyasa tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 25 ga watan Octoban da ta gabata.