Kungiyar manyan ma’aikatan jami’o’in Najeriya, SSANU da na kungiyar ma’aikatan jami’o’i NASU, a ranar Asabar, sun dakatar da yajin aikinsu bayan gajeren zama da suka yi da ministan Ilimi, Adamu Adamu a Abuja.
Ana sa ran janyewar zai fara aiki ne daga ranar Laraba na mako mai zuwa, Channels TV ta rahoto.
A cewar ministan ilimin, gwamnatin tarayya ta ware Naira biliyan 50 don biyan allawus na mambobin SSANU da NASU da na Kungiyar ASUU.
A Wani rahoton da ke fitowa daga jihar Zamafara ya bayyana cewa, ‘yan bindiga sun hallaka wani lauya mai suna B.T. Azza Esq.
Abokan aikinsa sun tabbatar da faruwar lamarin, sun kuma yi kira ga jami’an tsaro su yi bincike don gano makashin abokin su.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ta sake jaddada manufarta na kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wasu miygun ‘yan bindiga sun bindige lauya a birnin Gusau na jihar Zamfara a ranar Alhamis din da ta gabata.
Rahoton gidan talabijin na Channels ya bayyana cewa, ‘yan bindigan sun shiga gidan Barista Benedict Azza da ke unguwar Saminaka, a Gusau, inda suka yi yunkurin sace shi.
Majiya ta bayyana cewa, an lauyan ya yi gwagwarmayar shiga motarsa da nufin ya tsere, amma ‘yan bindiga suka harbe shi har sau uku.
Barrista Junaidu Abubakar, na kungiyar lauyoyin Najeriya reshen jihar Zamfara ya tabbatar da faruwar lamarin a yau Juma’a 19 ga watan Agusta.
Abokin sa ya ba da labarin yadda aka kashe shi Junaidu ya ce, an tsinci ganwar Barista ne a kusa ofishin jami’an hukumar kiyaye haddura ta kasa da ke kan titin bye-pass bayan tsagerun suka hallaka shi, rahoton jaridar Guardian.
A cewarsa: “Jiya da misalin karfe 12:30 na dare, ina gidana naga kiran wasu abokan aikinmu uku suna sanar da ni cewa wasu ‘yan bindiga sun harbe B.T. Azza Esq, kuma ga can gawarsa a kwance a bakin titi a hanyar bye-pass kusa da ofishin FRSC da ke Gusau.”
Da yake tabbatar da faruwar lamarin, mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara SP Mohammed Shehu, ya shaidawa majiyar cewa yanzu dai ana ta bincike don gano tushen mutuwar Barista.
Hakazalika, jami’in ya kara wa mazauna karfin gwiwar cewa, ‘yan sanda a fadin jihar sun dukufa domin tabbatar da kare rayukan mazauna.
Har Yanzu Ni Dan Gani Kashe Nin Buhari Ne, In Ji Fasinjan Da Aka Ceto Daga Jirgin Kasar Kaduna Zuwa Abuja.