Sri Lanka; An Umurci Sojoji Su Bindige Masu Tarnaki Ga Tsaro.
Ma’aikatar tsaro a Sri Lanka ta umurci sojojinta kasar da su bindige wadanda ke da hannu wajen kwasar ganima, a daidai lokacin da tashe tsahen hankula masu nasaba da rikicin siyasa a kasar ke kara kamari.
Mutane takwas ne aka rawaito sun suka mutu, kana wasu sama da 200 suka jikkata da suka hada da ‘yan sanda biyu, kana an farmawa gwamnan gine-gine ana ta kwasar ganima, tun fara rikicin mafi muni.
A halin da ake ciki dai masu bore a kasar suna neman shugaban kasar Gotabaya Raja-paksa da ya sauka daga mulki, wanda ke nufin murabus din da firaminsitan kasar ya yi bai gamsar da masu zanga zangar ba.
READ MORE : Enrique Mora Ya Ce Zai Ziyarci Iran Game Da Tattaunawar Vienna.
Firaministan kasar Mahinda Raja-paksa ya yi murabus ne bayan artabun da akayi tsakanin magoya bayansa da kuma masu zanga zangar ranar Litini.
READ MORE : Sojojin Isra’ila, Sun Bindige ‘Yar Jaridar Aljazeera A Yammacin Kogin Jordan.
READ MORE : Sojojin Isra’ila sun harbe shugaban jaridar Al Jazeera.