Sojojin Nijar da Burkina Faso Sun Kashe ‘Yan Ta’adda Kimanin 100 A Cikin Watan April.
Wani rahoton soji ya tabbatar da kashe ‘yan ta’adda kusan 100 a wasu hare-hare na hadin gwiwa da sojojin Burkina Faso da Nijar suka kai a cikin wannan watan Afrilu a kan iyakokin kasashen biyu.
Tashar Russia Today ta bayar da rahoton cewa, A cewar rahoton da aka gabatar a kasar Burkina Faso, tare da halartar Laftanar-Janar David Capri, babban hafsan hafsoshin sojojin Burkina Faso, da Kanar Salifou Modi, kwamandan sojojin Nijar, “dakarun kasashen biyu sun gudanar da aiki tare a wani farmakin hadin gwiwa, tsakanin ranakun 2 zuwa 25 ga watan Afrilu, tare da taimakon jirage marasa matuka.
Rahoton ya kara da cewa, an halaka ‘yan ta’adda kimanin 100 a yayin farmakin, an kama akalla mutane 40 da ake zargi, an lalata ko kuma tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda, tare da kama ko lalata makamai da alburusai, da kayayyaki da na’urorin da aka kera don tayar da ababen fashewa, da kuma jarkuann man fetur da motoci.
Rahoton ya bayyana cewa, sojojin biyu sun rasa rayukansu a yayin harin, sannan kuma rundunonin sojin kasashen biyu sun kai kayayyakin abinci ga mazauna yankunan da aka gudanar da aikin na hadin gwiwa, tare da basu tallafin magunguna.