Dakarun Sojojin Najeriya sun yi nasarar kama wani hatsabibin dillalin bindigu da sunansa ke cikin wadanda ake nema ruwa a jallo.
Manjo Janar Benard Onyeuko, Kakakin Rundunar Sojojin Najeriya ne ya sanar da hakan yana mai cewa a Jihar Taraba aka kama shi Onyeuko ya kara da cewa sojojin sun kama wani dan bindiga mai shekara 65 mai suna Ichen Igbaka da matarsa Salomi Gbaka.
Dakarun Sojoji na Operation Whirl Stroke, ta ce ta kama wani hatsabibin dilallin bindigu, Ardo Manu Abdulrahaman Maranewo, wanda jami’an tsaro ke nema a jallo.
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa an kama shi ne a Jihar Taraba.
Sojoji Najeriya Sunyi Nasarar Kama Mai Sayarwa Yan Ta’adda Bindigu Da Ake Nema Ruwa A Jallo.
An kashe akalla mutum 16 a sabon harin da aka kai jihar Benue Direkatan Sashi Watsa Labarai na Sojoji, Manjo Janar Benard Onyeuko, wanda ya bayyana hakan a jiya a Abuja, ya ce Marenewa ya kware wurin sayarwa da bada hayan bindiga ga yan bindiga da masu garkuwa.
Ya yi bayanin cewa dakarun sojojin sun kai samame mabuyar yan ta’adda da ke a Maraba a Ukyonugu Ityuluv a karamar hukumar Ukum a Jihar Benue.
Sojoji sun kama dan bindiga mai shekara 65 Onyeuko ya bayyana yadda sojojin suka kuma kama wani dan bindiga mai shekara 65 mai suna Ichen Igbaka da matarsa Salomi Gbaka.
Ya kuma ce sojojin na FOB Bakura na Operation Hadarin Daji sun amsa kirar neman dauki daga Rain Dankura a karamar hukumar Bakura a Jihar Zamfara suka yi musayar wuta da yan bindiga bayan sun sace wasu fararen hula.
“Bayan artabun, yan bindigan sun ceto fararen hula guda shida suka kuma kashe yan ta’adda biyu.
An Kama Matar Ɗan Bindiga a Katsina Da N2.4m, Mijin Ya Tsere Ya Bar Ta A wani labarin, yan sanda a jihar Katsina sun kama wata matar aure, Aisha Nura, mai shekaru 27 dauke da kudi Naira miliyan 2.4 na cinikin makamai da aka sayarwa yan bindiga, The Punch ta ruwaito.
An kama Aisha, da aka ce matar dan bindiga ne, a ranar 25 ga watan Yuli a yayin da ta ke shirin hawa kan babur din haya (acaba) daga Batsari zuwa kauyen Nahuta.
Mai magana da yawun yan sandan jihar Katsina, SP Gambo Isah, ya tabbatar da hakan a ranar Juma’a.