Rundunar Sojin Sama ta Najeriya ta kuɓutar da mutum 26 da aka yi garkuwa da su yayin wani fatro a kan hanyar Birnin Gwari zuwa Kaduna ranar Laraba.
Kakakin rundunar, Air Commodore Edward Gabkwet, ya ce sun yi nasarar ce bayan dakarunsu sun hangi wasu motoci biyar babu fasinja a ciki a kusa da Anguwar Yako, abin da ke nuna akwai yiwuwar an yi garkuwa da su.
Wani direba ya faɗa wa BBC Hausa cewa an harbe wani fasinjansa lokacin da ‘yan fashin suka tare hanyar da misalin ƙarfe 9:00 na safiyar Laraba.
“Sojojin sun zo sun tambaye mu inda ɓarayin suke kuma mun nuna musu. Suna tsaka da yin harbe-harbe kuma sai ga mutane suna fitowa daga daji,” a cwaer wani direban daban.
Matafiyan sun bayyana cewa an faɗa musu an ga gawar wata mace a cikin daji, sannan wata mata ta yi ƙorafin cewa an kashe mijinta tana roƙon a taimaka mata a ɗauko gawarsa a dajin.