Sojojin Mali Sun Zargi Takwarorinsu Na Faransa Da Yi Musu Leken Asiri.
Sojojin dake mulki a kasar Mali, sun zargi takwarorinsu na kasar Faransa da yi musu leken asiri da kuma neman bata musu suna.
Hukumomin na Bamako sun ce sun gano kutsen jiragen saman kasashen ketare musamman wadanda dakarun faransa ke amfani dasu har sau sama da hamsin a cikin kasar ba bisa ka’ida ba tun daga farkon wannan shekara.
Wannan dai na zuwa ne bayan wani bidiyo da rundinar sojin faransa ta fitar da aka dauka a kusa da sansanin sojin da faransa ta fice dake tsakiyar kasar ta Mali.
Hukumomin na Mali, sun ce abunda ke tabbatar da leken asirin da faransa ke yi wa sojojin kasar, shi ne kasancewar wani jirgi marar matuki na faransa a saman sansanin sojin Gossi a ranar 20 ga watan Afrilu nan, kamar yadda kakakin gwamnatin Malin, Kanal Abdoulaye Maïga, ya bayyana a cikin wata sanarwa.
READ MORE : Kyautata Alaka Da Isra’ila Da Kasashen Musulmi Ke Yi Babban Kuskure Ne.
Ya kuma leken asirin da dakarun na faransa sukayi ya nuna su ke da hannu a hotunan bogin da aka fitar inda ake sargin sojojin na Mali da kisan fararen hula domin bata musu suna.