Hukumomi a Mali sun tabbatar da mutuwar sojojin kasar 16 baya ga raunatar wasu 10 bayan da motar tawagar Sojin ta taka nakiyar gefen hanya a yankin tsakiyar kasar mai fama da hare-haren kungiyoyi masu ikirarin jihadi da kuma ‘yan bindiga a gefe guda.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, sojojin a bangarensu sun hallaka maharan 5 yayin musayar wutar.
Kasar Mali na ci gaba da fama da matsalar mayaka masu ikirarin jihadi da kuma ‘yan bindiga tun bayan barkewar rikicin shekarar 2012, bayan da masu ikirarin jihadin suka yi yunkurin kwace iko da mulkin kasar.
Rikicin na Mali zuwa yanzu ya hallaka mutane fiye da dubu 500 baya ga tilasta miliyoyi kaura daga yankunansu don tsira da rayukansu.
Ka zalika yanzu haka wasu sassa na kasar ta Mali na karkashin ikon mayaka masu ikirarin jihadi musamman daga gabashi.
A wani labarin na daban wani jirgin saman daukar kaya ya isa Mali da jirage masu saukar ungulu 4 da wasu makamai daga Rasha, kamar yadda ministan tsaron kasar, Sadio Camara ya bayyana.
Wadannan kayayyaki sun isa Mali ne a daidai lokacin da dangantaka tsakanin kasar da Faransa, wadda ke taimaka mata wajen yakar ta’addanci ke ci gaba da yin tsami, bisa rahotanin cewa Mali na shirin daukar sojojin haya daga Rasha.