Sojojin Dake Mulki A Sudan Sun Ce Sun Shirya Tattaunawa Domin Mika Mulki.
Shugaban gwamnatin rikon kwaryar soji a Sudan, Abdel Fattah Al-Burhan, ya jaddada cewa, kofar sojojin kasar a bude take domin shirya tattaunawa ta kasa da nufin cimma nasarar mika mulki ga gwamnatin demokaradiyya a kasar.
A yayin wata tattaunawar shugaban da aka watsa ta gidan talabijin na Sudan TV, Al-Burhan ya ce, sojojin kasar a shirye suke su gudanar da tattaunawa game da wa’adin mika mulki a kasar muddin aka cimma matsaya.
Ya ce, “Ko ni ko kuma hukumar sojojin kasar, babu wanda yake son dawwama a mulkin Sudan.
Sojojin zasu sakarwa fagen siyasar kasar mara da zarar an yi nasarar gudanar da zabuka ko kuma an cimma maslaha a kasar.”
Ya yi kiran a shiga tattaunawa wadda zata kunshi dukkan bangarorin kasar, amma ban da jam’iyyar National Congress Party, ta tsohon shugaban kasar Omar al-Bashir.