Gwamnatin jihar Kaduna arewacin Nigeria ta fitar da rahoton kwamitin nan na shari’a wanda ya binciki rikicin da ya afku tsakanin ‘yan kungiyar Islamic Movement ta mabiya mazhabar Shi’a da sojojin kasar a Zaria.
Rahoton ya ce sojoji sun yi wa ‘yan Shi’a 349 kisan gilla, kuma gwamnatin Kaduna ta binne ‘yan Shi’a 347 a wata makabarta.
Rahoton — wanda gwamnatin jihar ta karba a ‘yan makwannin da suka gabata — ya kunshi abubuwan da suka wakana a ranar 12 zuwa 14 ga watan Disambar shekarar 2015 tsakanin sojoji da ‘yan Shi’a.
Bugu da kari, rahoton ya ce sojoji sun lalata wasu dukiyoyi na ‘yan Shi’a da suka hada da rushe gidan shugabansu, Ibrahim Alzakzaky, da cibiyar Husainiya, da kuma makarantar Fodiya.
Sai dai a wani sako da kakakin rundunar sojin kasa na Najeriya, Kanar Sani Usman Kuka-sheka ya aike wa BBC, ya ce za su yi raddi kan rahoton nan gaba kadan.
Kwamitin ya ce ya kamata a hukunta sojojin da suka kashe ‘yan Shi’a, sannan a dauki tsauraran matakai kan kungiyar ta ‘yan uwa Musulmi saboda keta dokoki da suke yi.
Ratohon ya ce soja daya ya ya rasa ran sa a rikicin.
Ya kuma zargi gwamnatin Nigeria da ta Kaduna da yin sakaci har kungiyar ta ‘yan Shi’a ta yi karfin da za ta iya zama wata barazana.
Rahoton ya kuma kunshi shawarwari ga gwamnatin tarayya da kuma gwamnatin jihar Kaduna a bisa yadda za a guji afkuwar irin wannan matsala a nan gaba.
Kazalika rahoton ya soki shugaban na kungiyar ‘yan uwa musulmi Ibrahim Alzazzaky da kin taka wa ‘yan kungiyar birki a lokacin rikicin.
Sai dai kungiyar ta ‘yan uwa musulmi ta yi watsi da rahoton, inda ta ce an kashe mata kusan mutum dubu daya.
Mai magana da yawun kungiyar Ibrahim Musa ya ce suna so a hukunta babban hafsan sojojin Nigeria Laftanar Janar Yusuf Tukur Burutai, domin a cewar su yana da hannu a kisan.