Zakakuran sojoji rundunar Operation Hadin Kai da Operation Desert Sanity, sun ragargaza manyan kwamandojin Boko Haram/ISWAP Lamarin ya faru ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Yulin 2022 a kan babbar hanyar Dikwa zuwa Gamboru dake jihar Borno Kamar yadda shafin rundunar sojin kasa ya bayyana a Twitter, sojoji sun yi nasarar kwace miyagun makamai daga mayakan ta’addancin.
Sojoji rundunar Operation hadin kai a cigaba da yaki da ta’addancin da suke yi tare da hadin guiwar Operation Desert Sanity, sun halaka manyan ‘yan ta’addan Boko Haram/ISWAP da suka hada da manyan kwamandojinsu a jihar Borno.
A shafin rundunar sojin kasan na Twitter, su sanar da wannan cigaban da aka samu a ranar Alhamis, 7 ga watan Yulin 2022 a kan babbar hanyar Dikwa zuwa Gamboru a jihar.
A wani labarin na daban mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma Shugaban Jama’atu Nasril Islam (JNI), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya bukaci gudanar da addu’o’i na musamman da Allah Ya kawo dauki kan kalubalen rashin tsaro da ke addabar al’uma.
A wata sanarwa da babban sakataren JNI, Dakta Khalid Abubakar Aliyu, ya fitar ranar Alhamis a Kaduna, Amirul Muminin ya kuma bukaci alhazan Nijeriya da su yi wa Nijeriya da shugabanninta addu’a na musamman, yayin da suke tsaye a kan dutsen Arafat.
Sanarwar ta kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su nemi taimakon Allah domin samun kwanciyar hankali, tsaro da zaman lafiya da ci gaban Nijeriya a daidai lokacin da babban zaben shekarar 2023 ke gabatowa.
JNI, ta sake nanata bukatar yin addu’o’i sosai domin samun sauye-sauyen siyasa cikin lumana, da kuma kawo karshen kalubalen zamantakewa da tattalin arziki iri-iri a kasar.
Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Idan aka yi la’akari da cewa al’amura guda biyu suna haduwa a ranar Juma’a, wato gobe akwai bukatar tunatar da musulmi da su yi azumin ranar 9 ga watan Zul-Hijja (Arafat), kamar yadda Annabi (SAW) ya koyar da shi. kasancewarta rana ta musamman ta Juma’a kuma ita ce mafificiyar ranar mako, a cikinta ake yin Sallar Juma’a da amsa addu’o’i a cikin sa’a ta musamman da Arafat – mafi kyawun ranar shekara a cikinta. Allah mai rahama yana gafartawa bayinsa kuma yana amsa dukkan addu’o’in ranar Arafat.
“Don haka Mai Martaba Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ya bukaci al’umar Musulmin Nijeriya da su azumci ranar, kamar yadda Manzon Allah (SAW) ya koyar kuma a yi addu’a neman Allah Madaukakin Sarki da ya shiga lamuranmu.