Dakarun rundunar sojoji sun kai samame kan mayakan kungiyar ta’addanci ta sama da kasa a jihar Borno.
Sojoji sun yi yayyafin bama-bamai a kan yan Boko Haram a yankin Banki da ke karaWadannan mar hukumar Bama lamarin da ya kai ga murkushe mayaka da dama.
An kai samamen ne bayan rahotanni sun tabbatar da wani wuri da masu tayar da kayar bayan ke amfani da shi a matsayin mabuyarsu yayin kai hari.
Wani samame da rundunar sojin Najeriya ta kai kan Boko Haram ta sama da kasa yayi sanadiyar mutuwar mayakan kungiyar ta’addancin da dama a Banki, karamar hukumar Bama ta jihar Borno, Zagazola Makama ya rahoto.
An tattaro cewa kungiyar Boko Haram ta sake yin gagarumin asara na mayakanta a harin da ya wakana a ranar 16 da 17 ga watan Nuwamban 2022 a mabuyar yan ta’addan da ke Chongolo da Tangalanda.
Jirgin yakin sojoji ya murkushe yan Boko Haram 16 Ruwan bama-baman da jirgin yaki na Super Tukano yayi ya sauka a inda suka yi nufin kai harin wanda yayi sanadiyar murkushe yan ta’addan su 16 da wasu baburansu.
Wata majiyar sirri ta fadama Zagazola Makama, kwararre kan lamarin tsaro a tafkin Chadi cewa wani harin da aka kai ta sama ya murkushe yan ta’adda da dama a kauyen Chongolo.
Majiyoyin sun bayyana cewa an kaddamar da aikin ne bisa bayanan sirri da ya nuna mayakan na amfani da wajen a matsayin mafaka inda daga nan suke kai farmaki ga sojoji da sauran wadanda suke hari a yankin Banki gaba daya.
Sojoji sun murkushe manyan yan bindiga a Zamfara Mun kawo a wani rahoto na daban cewa dakarun sojoji na Operation Hadarin Daji sun murkushe wasu kasurguman yan ta’adda uku da suka addabi al’umma a jihar Zamfara.
Sojojin Najeriya sun yi nasarar halaka Halilu Buzu, Yellow Kano da Alhaji Gana a wani farmaki da suka kai don kawar da masu tayar da kayar baya a yankin karamar hukumar Maradun ta jihar Zamfara.
Har ila yau, dakarun sojin sun tarwatsa wani wuri da kasurguman yan bindigar ke amfani da su wajen boye kayayyaki da muggan makamai da suke amfani da su wajen addabar al’umma.
Source:Legithausa