Sojoji sun gano wurin haɗa bindiga a kudancin Kaduna
Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta gano wani wurin haɗa bindiga a garin Kafanchan da ke karamar hukumar Jema’a na jihar Kaduna.
Wata sanarwa da hedkwatar sojin Najeriyar ta wallafa a shafinta na Twitter, ta ce ta gano wurin ne bayan gudanar da wani binciken sirri na tsawon mako ɗaya, inda ta samu nasarar kama wani da ake zargi da safarar bindigogi wanda aka daɗe ana nemansa ruwa a jallo.
Sojojin sun ce wanda ake zargin ne ya jagorancesu zuwa wurin da ake haɗa bindigogin, inda kuma aka cafke wani mutumi a wurin wanda yake sayar da bindiga kowace iri.
Har ila yau, sojojin sun ce wanda yake sayar da bindigogin ya amsa cewa ya ɗau tsawon shekaru biyar yana harkar safarar bindigogi, musamman ma a jihohin Kaduna da Filato.
Binciken sojojin ya kai ga ƙwato makamai daban-daban har guda 22 da suka haɗa da kananun bindigu bakwai, bindiga kirar AK 47 na gida guda biyu.
Sauran sun haɗa da bindigar submachine guda ɗaya da harsasai na musamman na 7.62mm.
Haka ma, a wani samame da sojojin suka yi a tsakar daren jiya, 22 ga Satumba, 2023, a kauyen Adua da ke Kafanchan, sun ƙwato bindigogin AK-47 guda biyu da wayoyin hannu biyu da rigunan ƴan sanda biyu da wandon soja ɗaya da sauransu.