Sojoji sun sami nasarar ƙuɓutar da wasu mutane da yan bindiga suka yi niyyar sace wa a ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna.
Kwamishinan tsaro na jihar, Samuel Aruwan, ya tabbatar da kuɓutar da mutanen, yace mafi yawancin su matan aure ne.
Yace wani jirgin yaƙin rundunar sojin sama ne ya kuɓutar da su yayin da ya gano yan bindigan kuma ya tsorata su har suka gudu suka bar mutanen. Jami’a rundunar sojin sama sun kuɓutar da wasu mutane da yan bindiga suka sace a ƙaramar hukumar Igabi, jihar Kaduna, kamar yadda Channels tv ta ruwaito.
Mutum Biyu Yayin da yake tabbatar da lamarin a wani jawabi da ya fitar, kwamishin tsaro da al’amuran cikin gida, Samuel Aruwan, yace yan bindigan sun kai hari ƙauyukan Najaja da Kerawa dake ƙaramar hukumar Igabi inda suka tasa ƙeyar mutane da dama mafi yawansu mata ne.
Yace lokacin da yan bindigan ke ƙokarin tafiya da mutanen da suke shirin sacewa ne, wani jirgin yaƙin sojin sama da ya fito sintiri a yankin ya gano su.
A dai-dai lokacin da jami’an sojoji dake cikin jirgin suƙa gano su, sai suka gargaɗe su kan zasu buɗe musu wuta, hakan ya tsorata yan bindiga sun tsere zuwa cikin daji.
Kwamishin yace: “Wasu yan bindiga sun kai hari ƙauyukan Najaja da kerawa inda suka yi ƙoƙarin sace mutane da dama kuma mafi yawancin su mata ne.”
“Bayan kai hari ƙauyukan, yan bindigan sun tasa mutane da yawa zuwa bayan gari a ƙoƙarinsu na sace su, amma sai wani jirgin yaƙin rundunar sojin sama da ya fito sintiri ya gano su.”
“Yayin da jami’an dake cikin jirgin suka gano yan bindigan, sai suka musu barazanar zasu buɗe musu wuta, hakan ya tsoratar da maharan suka gudu zuwa cikin daji suka bar mutanen a nan.”
Mr. Aruwan yace yan bindigan sun harbi wani matashi, Hamza Ibrahim, lokacin da suke ƙoƙarin tafiya da mutane a ƙauyen Najaja.
A wani labarin kuma Buratai Yayi Jimamin Mutuwar COAS Attahiru, Yace Marigayin Ya Ɗakko Hanyar Murƙushe Matsalar Tsaro Tsohon shugaban rundunar soji, Tukur Buratai, yayi alhinin rasuwar Janar Ibrahim Attahiru a hatsarin jirgin sama, kamar yadda Premium times ta ruwaito.
Buratai yace magajin nasa ya ɗakko hanyar da zai sanya Najeriya alfahari a ɓangaren tsaron da take fama da shi.