Rundunar sojin Najeriya ta ce ta yi nasarar kashe ɓarayin daji masu kai hare hare-hare da satar mutane 128 a arewa maso yammaci da kuma da ƴan Boko Haram 140 a arewa maso gabashin ƙasar.
Rundunar sojin ta bayyana haka ne cikinhttps://nigeria21.com/hau wata sanarwa da mai magana da yawunta Bernard Onyeuko ya fitar inda ya bayyana irin nasarorin da ayyukan rundunonin sojin suka samu a sassan Najeriya da ke fama da matsalolin tsaro.
Rundunar ta ce alƙalumman sun shafi ayyukan rundunoninta na tsawon mako biyu daga ranar 11 ga Nuwamba zuwa 25 ga watan.
Sanarwar ta ce an yi wa sansanonin ƴan bindiga da ƴan Boko Haram ruwan wuta da kama wasu daga cikinsu.
Sai dai rundunar sojin ba ta bayyana yawan jami’anta da aka kashe ba a yaƙin da ƴan bindiga a arewa maso yammaci da kuma arewa maso gabashi da sauran sassan Najeriya da ke fama da matsalar tsaro.
Wannnan na zuwa ne bayan shugaba Muhammadu Buhari ya ba manyan hafsoshin tsaron ƙasar umarnin fatattakar ƴan bindigar da ke kan hanyar Kaduna zuwa Abuja saboda ƙaruwar yawaitar hare-hare a sassan ƙasar,
Rundunar sojin Najeriyar ta ce, rundunar Hadin Ki ta kaddamr da hare-hare ta sama da kasa a maɓuyar mayaƙan Boko Haram da ISWAP a garin Baga na jihar Borno, mai iyaka da tafkin Chadi.
Ta ce an yi nasarar tarwatsa masu tada kayar bayan sakamakon samun bayanan sirrin cewa wasu daga cikin mayakan kungiyoyin biyu sun isa tafkin Chadi a kwale-kwale.
Rundunar ta ce a farmakin da ta kai yankin Askira Uba, an kashe sama da mayaƙan Boko Haram 50, an kuma yi nasarar kwace wasu daga cikin makamansu, ciki har da ma’ajiyar albarusai, da manyan motocin yaƙi da sauran makamai.
“Ƴan bindiga na ƙona mana amfanin gona idan ba mu ba su kuɗi ba”
Rashin tsaro: Manyan dazukan da ƴan ta’adda ke samun mafaka a arewacin Najeriya
Har wa yau, sojoji da ke garin Baga, sun yi nasarar kama wani kasurgumin dan ta’adda mai suna Haladu Saleh, wanda jami’an tsaro ke nema ruwa a jallo tun a shekarar 2018.
Sannan a wuraren binciken ababen hawa a Bukarti da Yusufari da kuma Maima Hari a hanyar Biu zuwa Damboa, an kama wani da ake zargi da kai wa ‘yan ta’adda kayayyaki bayan samun bayanan sirri da ke cewa ‘yan ta’addan na fakewa a kauyen Karawa.
An yi nasarar cafke Mista Ezekiel Karson da Galadima Bako wadanda ke kai wa ‘yan ta’addan muggan kwayoyi ciki har da tabar Wiwi.
A lokacin wannna aiki an kashe sama da ‘yan ta’adda 90, da cafke wasu 50.