Rundunar Soji a Najeriya ta sako mutum 13 da ake zargi da alaka da Boko Haram a Kano.
Kamar yadda soji suka bayyana, an sako su ne bayan ganewa da aka yi basu da alaka da ‘yan ta’addan.
Wasu daga cikinsu sun kwashe kwanaki 12 a hannun soji da jami’an hukumar tsaro ta farin kaya Mutane 13 da aka kama a jihar Kano saboda zarginsu da ake da zama ‘yan Boko Haram an sako su bayan bincike ya nuna cewa basu da wata alaka da kungiyar ta’addancin.
An kama wadanda ake zargin ne a wurin Masallacin Sheikh Sharrif Ibrahim Saleh dake Hotoro, karamar hukumar Tarauni ta Kano a ranar Asabar, 8 ga watan Mayun 2021.
A sako wadanda ake zargin daya bayan daya bayan kammala bincikensu. Wadanda aka saka na karshe sun kwashe kwanaki 12 a hannun jami’an tsaro kuma an sako su a ranar Laraba, 19 ga watan Mayun 2021.
Matar daya daga cikin wadanda aka sako ta ce mijinta ya dawo gida ne bayan kwashe kwanaki hudu da yayi a hannun rundunar sojin Najeriya, HumAngle ta ruwaito. Ta ce ana kama shi yayin da yake gudu zuwa gida daga masallaci.
Jami’an tsaro suka kira shi inda suka hada shi da sauran wadanda ake zargi, in ji matar da bata bada sunanta ba. Kamar yadda tace, wasu daga cikin wadanda aka kama an adana su ne a hukumar tsaro ta farin kaya a Kano kuma ana bincikarsu.
Wata matar daya daga cikin magidantan da aka sako ta nuna jin dadinta akan sako mijinta da aka yi kuma tace bata bacci lokacin da mijinta yake tsare. Tayi kira kira ga rundunar sojin Najeriya da su kiyayi tsare mutane ba tare da wasu dalilai ba.
Daya daga cikin wadanda aka sako ya mika godiyarsa ga Allah kuma yace baya son magana da ‘yan jarida tunda yanzu ya samu ‘yancinsa.
A wani labari na daban, a ranar Talata 18 ga watan Mayu, Gwamna Abdullahi Sule ya gabatar wa sarakunan gargajiya 25 na ajin farko a jihar Nasarawa da sabbin motocin SUV.
Jaridar Premium Times ta rahoto cewa idan har an sayi motocin ne kai tsaye daga kamfanin da ya kera su, za a kiyasta farashin su kan sama da Naira miliyan 800.
Sule ya gabatar da makullan sabbin Lexus 25 ga sarakunan a gidan gwamnati da ke Lafiya domin bikin cikarsa shekaru biyu akan karagar mulki.