Mai magana da yawon ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana a yau Lahadi cewa, kasar Sin ta bukaci bangarori biyu da ke rikici da juna a kasar Sudan, da su hanzarta tsagaita bude wuta tare da kaucewa barkewar rikici.
Ya kara da cewa, Sin na fatan dukkan bangarorin za su karfafa yin shawarwari da ciyar da tsarin mika mulki ta hanyar siyasa gaba cikin hadin gwiwa.
A jiya ma kwamitin tsaron MDD ya nuna matukar damuwa kan arangamar da aka yi tsakanin dakarun sojin Sudan da na RSF, inda ya bayyana nadama kan asarar rayuka da aka yi.
A cikin wata sanarwa da suka fitar, mambobin kwamitin sulhun sun bukaci bangarorin da su gaggauta tsagaita bude wuta, su kuma kwantar da hankula tare da yin kira ga dukkan bangarorin da su koma ga teburin tattaunawa domin warware rikicin kasar.
Shi ma shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka (AU) Moussa Faki Mahamat, ya yi kira da a tsagaita bude wuta a kasar Sudan, a daidai gabar da ake gwabza fada tsakanin sojojin Sudan da RSF, a cewar wata sanarwa da kungiyar ta fitar jiya Asabar.
A jiya ne dai rikici ya barke a birnin Khartoum, babban birnin kasar Sudan, da kuma wasu yankuna, bayan da aka shafe kwanaki da dama ana takun saka tsakanin dakarun RSF da sojojin kasar. Rundunar RSF ta yi ikirarin cewa, dakarunta sun kwace wasu muhimman wurare a babban birnin kasar, ciki har da filin jirgin sama