Shugabannin Fulani makiyaya da ke kudu maso yammacin Nijeriya sun yi wata tattaunawa domin nemo mafita kan dokar hana kiwo a fili da wasu jihohin yankin kudu suka yi.
An gudanar da taron ne a yau Lahadi a fadar sarkin Fulanin jihar Legas, Alhaji Muhammadu Abubakar Bambado dake a Surulere a Legas.
Shugabannin makiyayan sun yi shirin bin wannan doka sau da kafa da hukumomin yankin suka sanya, tare da shirin nemo wasu hanyoyin kiwo na daban. Gwamnonin yankin kudu sun yi wata doka domin hana Fulani kiwo a fili da kuma a dazuka.