Shugaban yan ta’adda ya kashe daya daga cikin mabiyan shi.
Hukumar yan sanda ta Katsina na gudanar da bincike akan wani shugaban yan ta’addan daya kashe daya daga cikin mabiyansa bayan ya kashe mutumi da sukayi garkuwa da shi.
Yan ta’addan su bakwai ne suka shiga gidan Umar Abdullahi dake karamar hukumar faskari wanda yaki amincewa ya bisu har ta kaida daya daga cikin yan ta’addan, Abdullahi Iliya ya aikashi lahira.
Shugaban yan ta’addan, Yellow ya fusata inda shima ya aiki Iliya lahira. Mai magana da yawun yan sanda SP Gambo Isah ya bayyana cewa an kama mutane biyu da ake zargi akan lamarin masu suna Nasiru Muhammad da Abubakar Ikiyasu.
READ MORE : Saudiya Da, UAE Sun Ki Amsa Kiran Wayen Biden Kan Tsadar Farashin Mai A Kasuwannin Duniya.