Shugaban Najeriya Ya Kama Hanyar Zuwa Birnin London Don Duba Lafiyara.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN shi ne ya kawo rahoton inda ya nuna cewa shugaban kasar ya shirya wucewa kasar Ingila ne daga wajen taron daya halarta kan kare mahalli a birnin Nairobi na kasar Kenya, kamar yadda Kakakin shugaban kasar Femi Adesina ya bayyanawa manema labarai
Sai dai daga bisani shugaban ya dawo gida Abuja, kafin kama hanyarsa zuwa kasar birtaniya domin duba lafiyarsa, daga lokacin da aka ranstar dashi a matsayin shugaban kasa na farar hula buhari ya yi tafiye tafiye zuwa kasar birtaniya domin duba lafiyarsa kan cutar da har yanzu ba’a bayyanata ba ga yan Najeriya.
Kafin kafin kama hanya zuwa birtaniya shugaba Buhari ya bayyana cewa mataimakina Frofeso Yemi Osinbanjo ne zai ci gaba da kula da harkokin mulkin kasar tare da taimakon sakataren gwamnati Boss Mustapha da kuma shugaban Ma’aikatan fadar shugaban kasa.
Ya zuwa yanzu dai babu wani abin da ke nuna cewa shugaban ya aike da wasika zuwa ga majalisa ta mika ragamar jagorancin kasar ga mataimakinsa Osinbanjo idan baya nan, kamar yadda kundin tsarin mulkin kasa ya tanada ayi.