Shugaban Kasar Kenya Ya Nuna Goyon Bayansa Ga Raila Odinga A Zabe Mai Zuwa.
Makwanni kadan bayan da jam’iyyunsu su ka kulla kawance, Kenyatta ya nuna cikakken goyon bayansa ga tsohon abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasar da za a yi a watan Ogusta mai zuwa.
Shugaba Uhuru Kenyatta wanda ya gabatar da jawabi a gaban daruruwan magoya baya a birnin Nairobi , ya fadi cewa; “ Mun zabi Raila Odinga”
Makwanni biyu da su ka gabata ne dai jam’iyyun biyu na shugaban kasa da na Raila Odinga su ka kulla kawance domin fuskantar zaben da za a yi na shugaban kasa da na ‘yan majalisa.
Jam’iyyar Kenyatta ta Jubilee Party, da ta Odinga Orange Democrati, sun daga taken; “ Kishiruwa Domin Hadin Kai” domin dinke hamayyar da yake a tsakaninsu ta tsawon shekara da shekaru a fagen siyasa.
READ MORE : Kasar Yemen Ta Yi Tir Da Zartar Da Hukuncin Kisa Da Saudiyya Ta Yi.
A zaben da aka yi a 2017 wanda jam’iyyun biyu su ka yi hamayya da juna a zaben shugaban kasa, an kare da fadace-fadace da ya dauki salon kabilanci da zubar da jinin mutane da dama.
Odinga ya tsaya takarar shugaban kasa a shekarun, 1997, 2007, 2013 da 2017. Wannan karon zai zamar masa karo na biyar.