Shugaban PDP a shiyyar Kaduna ta tsakiya, Shehu Ahmed Giant, ya riga mu gidan gaskiya da safiyar Talatan nan 13 ga watan Disamba, 2022.
A wata sanarwa da Usman Muhammad Gwarzo ya fitar yace marigayin, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa ya rasu ne a Asibitin 44.
Ya kuma bayyana cewa an shirya za’a masa Sallar jana’iza a Masallacin Sultan Bello bayan sallar Azuhur yau Talata.
Da safiyar Talatan nan 13 ga watan Disamba, 2022 muka samu labarin rasuwar shugaban jam’iyyar PDP na shiyyar Kaduna ta tsakiya, Shehu Ahmad Giant.
Marigayi Shehu Giant, tsohon shugabar ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa, ya ce ga garinku nan ne a Asibitin Sojojin Najeriya na 44 dake cikin birnin Kaduna.
Sanarwan tace: “Kowane mai rai mamaci ne, Innalillahi wa Inna Ilaihi Raji’un, ba da jimawa ba Honorabul Shehu Ahmad Giant, tsohon shugaban ƙaramar hukumar Kaduna ta arewa kuma shugaban PDP na shiyyar Kaduna ta stakiya ya rasu.”
Sanarwan ta ƙara da cewa za’a yi wa marigayin gata na karshe watau Sallar Janaza da kuma kai shi makwancinsa bayan Sallar Azahar a Masallacin Sultan Bello yau.
Sanarwan ta ci gaba da cewa: “Muna Addu’a Allah SWT ya sa gidan Aljannatul Firdausi ya zame masa makoma ta karshe bayan rasuwarsa.
Za’a yi jana’izarsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna bayan Sallar Azuhur.”
Bayanai sun nuna cewa kafin rasuwar marigayi Shehu Ahmed Giant ya jima yana fara da rashin lafiya da ta kai ga kwantar da shi a Asibiti don zama karkashin kulawar Likitoci.
A wani labarin kuma kun ji cewa ɗan takarar majalisar tarayya daga jihar Osun karkashin inuwar PDP a 2023, Mista Sola Arabambi, ya kwanta dana.
Wani makusancin ɗan siyasan wanda ya nemi a sakaya bayanansa yace Uban gidansa ya rasu ne ranar Asabar, 3 ga watan Disamba, 2022 bayan fama da rashin lafiya ta ƙankanin lokaci.
Tuni dai yan uwa da abokanan arziki da abokan siyasa suka fara tururuwar tura sakon ta’aziyya ga iyalan marigayin da jam’iyyar PDP baki ɗaya.