Shugaban hafsun sojan kasa, Laftana Janar Ibrahim Attahiru, ya mutu yau – Janar Ibrahim Attahiru ya cika ne bayan ya yi hadari a jirgin saman sojoji.
Wannan mummunan hadari da ya rutsa da mutane 9 ya auku ne a Kaduna Labari ya na zuwa mana cewa shugaban hafsun sojojin kasa na Najeriya, Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya rasu dazun nan.
Mabanbantan rahotanni sun tabbatar mana da mutuwar babban sojan kasar wanda ya shiga ofis a karshen Junairun 2021. Jaridar PM News ta bayyana cewa Laftana Janar Ibrahim Attahiru ya mutu a sanadiyyar hadarin jirgin sama a ranar Juma’a.
Majiyar ta ce jirgin da ya dauko Janar Ibrahim Attahiru zuwa garin Kaduna ya gamu da hadari a filin sauka da tashin jirage. Marigayin ya rasu ne tare da wasu daga cikin hadimansa, wanda kawo yanzu ba a tantance su ba.
Daily Trust ta tabbatar da aukuwar wannan mummunan labari dazu, amma ba ta samu cikakken rahoton yadda abin ya auku ba.
Rundunar sojojin sama na kasa ta ce an samu wani hadarin jirgin sama a kusa da filin sauka da tashin jirage da ke garin Kaduna.
A shafinta na @NigAirForce a Twitter, rundunar sojojin saman ta bada wannan sanarwa ba tare da fadin wadanda aka rasa ba.
“Wani hadarin jirgin sama da ya shafi jirgin @NigAirForce da yammacin nan a kusa da babban filin jirgi na Kaduna ya auku.”
“Ana binciken abin da ya yi sanadiyyar wannan hadari. Za a samu karin bayani nan gaba.” Darektan yada labarai da hula da jama’a a rundunar sojojin saman Najeriya, Edward Gabkwet, ya sa hannu a wannan sanarwar.
Mutane akalla takwas ake zargin sun mutu tare da Shugaban sojin Ibrahim Attahiru mai shekara 54 wanda ya canji Janar Tukur Buratai kwanaki.
A baya an ji cewa rundunar Sojojin Najeriya ta rasa jami’ai akalla uku hannun miyagn ‘Yan bindiga a kauyen Mariga, jihar Neja.