Jaridar Daily Trust tace a lokacin shugaban hukumar EFCC ya rufe fuskar sa inda ya nemi gafarar cewar ba zai iya ci gaba da bayani ba, abinda ya sa ministan sadarwa Isa Ali Pantami ya taimaka masa komawa kujerar sa.
Wannan ya sa aka ruga da Bawa zuwa sibiti fadar shugaban kasa, daga bisani kuma aka sanar da cewar yana cikin yanayi mai kyau.
Hukumar EFCC ta sanar a shafin ta cewar Bawa ya murmure kuma nan bada dadewa ba zai koma ofishin sa domin ci gaba da gudanar da aikin sa.
Sanarwar tace lallai shugaban Hukumar ya gamu da rashin lafiya amma kuma ya warke.
Bawa na daga cikin mutanen dake fuskantar kalubale sosai a cikin jami’an gwamnatin Najeriya sakamakon aikin da hukumar sa keyi na kwato dukiyar jama’a daga wasu tosffin manyan jami’an gwamnati da ‘yan kasuwar suka yi rub da ciki da dukiyar talakawa.
Nadin sa akan mukamin da shugaban kasa Muhammadu Buhari yayi ya karfafa jama’ar Najeriya da dama a matsayin sa na matashi da kuma wanda ya girma a cikin hukumar sabanin jami’an ‘Yan Sandan da ake nadawa a baya.
Hukumar EFCC na da matukar tasiri wajen aikin yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, lura da irin makudan kudade da kadarorin da take kwatowa kowacce shekara.
Shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta Najeriya EFCC, AbduRashid Bawa, ya ce kawo yanzu hukumar tayi nasarar kwato dala miliyan 153 daga hannun tsohuwar ministar kula da albarkatun man fetur ta kasar Diezani Alison Madueke.
Bawa ya kuma ce akwai wasu shari’o’in dake gudana yanzu haka kan laifukan almundahanar makudan kudade a Najeriya, ciki har da batun cin han ci da rashawar kimanin dala miliyan 115 kan sha’anin zabe.
Tun cikin watan Fabarairun da ya gabata hukumar EFCC a karkashin tsohon shugabanta Ibrahim Magu, ke neman hukumomin Birtaniya, inda a can ma take fuskantar shari’a, da su miko mata Mis Diezani domin ta fuskanci shari’a akan tuhumar wawashe akalla dala biliyan 2 da rabi daga baitulmalin gwamnati.