Shugaban kasar congo na iya dawo da sojojin kasashen Turai Jamhuriyar Congo a karon farko cikin shekaru 14, biyo bayan shawarar da shugaba Felix Tshisekedi ya yanke ta gayyato dakarun Turan domin taimaka musu wajen yiwa ‘yan tawayen kasar kwaf daya.
A matakin farko dai, shugaban ya soma tuntubar kungiyar tarayyayr Turai EU ne kan bukatar soma baiwa dakarun Jamhuriyar Congo horo, batun da ministan tsaron kasar ya tattauna da jakadan kungiyar ta EU a birnin Kinshasa tun ranar Talatar da ta gabata.
Baya ga kungiyar kasashen Turai, shugaban gwamnatin Congo ya kuma shiga tattaunawa da makwafciyarta Uganda domin kafa wata rundunar sojin hadin gwiwa da za ta murkushe mayakan ‘yan tawayen kungiyar ADF, da suka kuntatawa lardin arewacin Kivu.
Sabon yunkurin gwamnatin Jamhuriyar Congo na zuwa ne, bayan rahoton majalisar dinkin duniya da ya ce a shekarar bara kadai, mutane 851 mayakan kungiyar ADF suka kashe a lardin na Arewacin Kivu.
Tun a farkon watan Mayun da muke, rundunar sojin Jamhuriyar Congo ta kaddamar da farmaki kan gwamman kungiyoyin ‘yan tawaye da na ta’addancin da suke rike da yankuna da dama a lardunan arewacin Kivu da kuma Ituri.
A wani labarin kuma shugaban Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo Felix Tshisekedi ya baiwa sojoji da ‘Yan sanda karbe ikon kula da Yankunan Arewacin Kivu da kuma Ituri sakamakon kwarya-kwaryar dokar ta bacin da ya kafa.
Shugaban yace ya saurari koke koken mazauna wadannan yankuna dake fama da matsalar tsaro musamman mata da Yam mata, saboda haka ya kawar da shugabannin fararen hular dake aiki a yankunan inda ya maye gurbin su da sojoji da kuma ‘Yan Sanda.
Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Tharsice Kasongo Mwemba yace daga ranar 6 ga watan nan wadannan yankuna guda biyu zasu shiga cikin dokar ta bacin na kwanaki 30, kuma za’a tafiyar da yankunan ne a karkashin dokar soji.
A farkon watan nan na Mayu Gwamnatin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo ta ayyana kwarya-kwaryar dokar ta – baci a larduna 2 dake gabashin kasar da kungiyoyi masu daukar makamai suka addabi al’umma.
Wani dan majalisar dokokin kasar, Patrick Muyaya ya shaida wa manema labarai cewa shugaban Felix Tshekidi ya bayyana wa majalisar shawarsa ta ayyana wannan kwarya-kwaryar dokar-ta-baci duba da yadda matsalar tsaro ta ki ci ta ki cinyewa a lardunan arewacin Kivu da Ituri.
Shugaban Jamhuriyar Demokradiyar Congo Félix Tshisekedi, yayin wata ziyara Faransa ranar 27 ga watan Afrilu 2021
A karkashin dokokin Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo, shugaban kasa na iya ayyana dokar ta baci ko kwarya kwaryar ta idan yanayin da ake ciki na barazana da yancin kasar ko mutuncinta.