Shugaba Buhari ya kaddamar da aikin hako man fetur a Arewacin Najeriya
Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya ya kaddamar da aikin hako man fetur a yankin Kolmani da ke tsakanin jihohin Bauchi da Gombe.
Yayin kaddamarwar shugaba Buhari ya umarci kamfanin mai NNPCL yayi duk mai yiwuwa a hurumin da doka ta bashi, don tabbatar da sun janyo masu zuba jari don bunkasa sarrafa man fetur a Arewacin Najeriya.
Haka kuma Shugaba Buhari ya ce ya tattauna da gwamnonin Bauchi da Gombe inda suka tabbatar masa da za su bayar da hadin kai don ci gaba da aikin bunkasa haƙo man fetur din.
Bayan Shugaba Muhammadu Buhari ya yi wannan kaddamarwa, BBC ta tattauna da daya daga cikin manyan Jami’an kamfanin mai na NNPC da ke kula da inda kamfanin ke zuba jari, Bala Wunti, inda ya shaida cewa an gano akalla ganga fiye da biliyan ɗaya ta danyen man fetur a karkashin kasa.
Kazalika ya ce ana fatan gina matatar mai da kamfanonin samar da taki da kuma iskar gas.
Matatar man da ake fatan ginawa za ta rika sarrafa ganga fiye da 100,000 a kullum.
Martanin Sana’a game da satar man kasar Yamen: Ba mu kara yin gargadi ba; Mun bugi tankar.