Gwamna Nyesom Wike ya koma gefe ya yi shiru a PDP, ya ki fitowa ya goyi bayan Atiku Abubakar Na kusa da Wike su na cewa ya zama dole ayi waje da Iyorchia Ayu daga kujerar shugaban Jam’iyya Takarar Atiku Abubakar na fuskantar barazana idan bai shawo kan ‘yan bangaren Gwamnan Ribas ba.
Rahoton Daily Trust ya bayyana cewa gum din da Nyesom Wike yake yi tun bayan zaben fitar da gwani, ya damalmala abubuwa a jam’iyyar PDP.
Rashin jituwar Gwamna Nyesom Wike da Atiku Abubakar ya na barka PDP a kudancin Najeriya. Bugu da kari Wike ya ki bari ya zauna da mutanen Atiku.
Manyan wadanda ke goyon bayan Gwamnan irinsu Okezie Ikpeazu, Seyi Makinde, Samuel Ortom, da Ayodele Fayose sun nuna fushinsu ga Atiku Abubakar.
Duk abin da ake yi, Wike ya yi tsit wanda hakan ta sa ake tunanin zai iya sauya sheka zuwa APC, LP ko NNPP, ko akalla ya ki taimakawa PDP a zaben 2023.
Kai ya rabu a PDP Kan kusoshin PDP a kudancin Najeriya ya rabu tun da Atiku ya tsaida Ifeanyi Okowa a matsayin mataimakinsa, wasunsu su na adawa da wannan zabin.
Rahoton Daily Trust ya nuna Atiku da Okowa na fuskantar barazana a jihohin irinsu Delta, Edo, Akwa Ibom, Bayelsa, Legas, Ogun, Ondo, Anambra zuwa Imo.
Amma a jihohin Ribas, Kuros Riba, Enugu, Abia, Oyo da Ekiti, ‘ya ‘yan PDP ba su gamsu da Okowa ba. Masana su na ganin hakan zai iya kawowa PDP cikas.
Ifeanyi Okowa tare da Atiku Abubakar Hoto: @IAOkowa Asali: Twitter Sai an tunbuke Ayu The Nation ta ce mutanen Nyesom Wike sun bukaci shugaban PDP na kasa watau Iyorchia Ayu ya sauka daga kujerarsa a matsayin sharadin farko na yin sulhu.
Ba dole ba ne ‘dan takaran da sauran ‘yan PDP su yarda a sauke shugaban jam’iyyar haka kurum. Idan abubuwa suka tafi a haka, Atiku Abubakar ba zai kai labari a a zabe mai zuwa a jihohin da suka fi ko ina yawan kuri’u a Najeriya ba; Ribas, Legas da Kano.
Bukola Saraki yana kokarin dinke barakar da ta taso, tsohon shugaban majalisar yana bi yana lallaban Wike da mutanen na sa, su marawa Atiku Abubakar baya.
Wasu tsofaffin gwamnoni da tsofaffin Ministoci da wadanda aka kafa PDP da su, duk su na goyon bayan Atiku, amma akwai bangaren da su na bayan Gwamnan ne.
Irinsu Tsohon Gwamnan Gombe, Ibrahim Hassan Dankwambo, tsohon Ministan shari’a, Mohammed Bello Adoke, ‘yan majalisu da-dama ba su tare da Atiku.
BOT ta tsoma baki Majalisar amintattu na BOT ta dauki mataki domin sasanta rigimar da ke neman barkewa a PDP.
A farkon makon nan aka tabbatar da wannan labari a wata sanarwa.