‘Yan bindigar da ke shan ragargaza a hannun sojojin Najeriya sun aike da wata wasika ga al’ummar Shinkafi ta jihar Zamfara, inda suka sanar da shirinsu na kai musu farmaki.
Dr. Sulaiman Shu’aibu Shinkafi, daya daga cikin dattawan Shinkafi da a halin yanzu yake zaune a birnin Abuja, ya shaida wa RFI Hausa cewa, lallai wannan wasika ta tayar musu da hankali, yana mai kira ga gwamnatin da ta ceto garin Shinkafi daga wannan musibar.
Muna kira ga gwamnatin tarayya da ta yi kokari ta taimaka wa bayin Allah da ke cikin garin Shinkafi da kewaye domin wannan wasika ta tayar mana da hankali. Inji Dr. Shinkafi.
Tuni dai gwamnati ta katse hanyoyin sadarwar wayar salula domin bai wa sojojin damar gudanar da ayyukansu na luguden wuta kan ‘yan bindigar yadda ya kamata.
A wani labarin na daban gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi nasarar gano tare da tsare wasu fitattun mutane da ake zargi da tallafa wa ayyukan ta’addanci a kasar kamar yadda Ministan Shari’a Abubakar Malami ya bayyana.
Mun toshe kafofi masu nasaba da samar da kudaden, sannan mun fara gudanar da gagarumin bincike wanda ke haifar da da mai ido a kokarin yaki da ta’addanci. inji Malami
Koda yake Malami ya ce, ba zai yi rika malam masallaci ba wajen zurfafawa a cikin bayanansa saboda a haklin yanzu ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin.
A cikin watan Mayun da ya gabata ne Malami ya ce, gwamnatin Najeriya na shirin fara tuhumar wasu mutane 400 cikinsu kuwa har da wasu fitattu da ake zargi da bai wa Boko Haram kudaden tallafi.
Sai dai an yi ta caccakar gwamnatin kan jinkirta tuhumar mutanen, amma Malami ya bada tabbacin cewa, gwamnatin tarayyar ta dukufa wajen daukar tsauraren matakan yaki da ta’addanci a kasar, yana mai bada da misali da irin nasarar da ake samu kan mayakan Boko Haram da kuma ‘yan bindiga da suka addabi kasar.