Shin hare-hare ƙaruwa suka yi ko raguwa a mulkin Tinubu?
Wani rahoto ya ce mutanen da aka kashe sanadin ayyukan taɓarɓarewar tsaro a Najeriya cikin Yuni, watan farko na mulkin Shugaba Tinubu, sun ƙaru.
Adadin mutanen da aka kashe ɗin ya kai 854.
Rahoton na kamfanin Beacon Consulting mai bincike kan harkokin tsaro a Sahel ya ce yawan ‘yan Najeriyan da aka kashe ya ƙaru da kashi 26.4%, idan an kwatanta da na watan Mayu.
Haka zalika yawan mutanen da aka sace a watan na Yuni ya ƙaru da kashi 35.1%, da adadin mutum 239, idan an kwatanta da mutum 168 da aka sace a watan Mayu.
Binciken na zuwa ne sama da mako uku bayan naɗa sabbin manyan hafsoshin tsaron Najeriya, ciki har da Mashawarcin Tsaro na Ƙasa, Mallam Nuhu Ribaɗu.
Kashe-kashen da sace-sacen mutanen sun faru ne a cewar Beacon Consulting cikin ƙananan hukumomin ƙasar 234.
Ya ce mutanen da aka kashe sanadin ayyukan rashin tsaron sun fi yawa a yankin Arewa maso Tsakiya, inda aka samu mutuwar mutum 281, sai kuma Arewa maso Gabas inda mutum 280 suka mutu.
A yankin Arewa maso Yamma kuwa, hare-haren ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro sun yi sanadin mutuwar mutum 145 a cikin watan na jiya.
Ya yi iƙirarin cewa kashi 82.6% na ɗaukacin kashe-kashen da aka yi a watan Yuni, sun faru ne a jihohin arewa.
Binciken ya kuma ce Borno ce jiha mafi yawan kashe-kashen mutane a cikin watan Yuni, inda hare-hare suka yi sanadin mutuwar 264. A jihar Kwara, an samu mutuwar mutum 111 a cikin Yunin.
Jihar Filato, adadin mutum 99 aka kashe sai Sokoto mutum 50 yayin da Zamfara ta samun yawan mutum 40 da aka kashe dalilin taɓarɓarewar tsaro a watan na jiya.
Ƙididdigar binciken mace-macen a cikin wata uku wato daga Afrilu zuwa ƙarshen watan Yunin 2023, matsalolin tsaro sun yi sanadin mutuwar mutum 2,240 a faɗin Najeriya.
A nan kuma, yankin Arewa maso Tsakiyar Najeriya ne aka fi samu yawan mutanen da kashe da adadin 737, sai yankin Arewa maso Gabas inda aka kashe mutum 587, a Arewa maso Yamma, an samu mutuwar 426.
Me ya janyo ƙaruwar kashe-kashe?
Rahoton Beacon Consulting ya ce yankunan Arewa maso Yamma da na Arewa ta Tsakiya, inda aka samu gagarumar matsalar tsaro da harkokin siyasa ciki har da miyagun laifuka daga ƙungiyoyi masu ɗauke da makamai.
Haka zalika, binciken ya ambaci ‘yan fashin daji da ƙungiyoyin masu aikata laifi da tashin-tashinar al’umma da rikice-rikicen ƙabilanci da kuma ƙaruwar ganin baiken juna tsakanin sabbin gwamnatoci da waɗanda suka gabace su kamar a jihohin Kano da Zamfara da kuma Sokoto.
Wani al’amari kuma shi ne hare-haren da ake kai wa a kan matafiya da ƙauyuka musamman a jihohi irinsu Kaduna da Sokoto da Neja da Katsina da Zamfara Kebbi da kumaKano ciki har da Babban Birnin Tarayya.
Rahoton ya ce mafi yawan matsalolin tsaron na da alaƙa da ‘yan bindigar da suka bazama bayan dakarun sojoji sun fatattake su daga sansanoninsu saboda ayyukan jami’an tsaro irinsu Operation Hadarin Daji da na Safe Haven da kuma Whirl Stroke.