Kafin ya bar Duniya, Abubakar Shekau ya fadi inda Boko Haram ke samun makamai.
A wani sako da ya shiga hannun ‘Yan jarida, an ji Shekau ya na wadannan bayanan A wani bangare na sakon sautin da Abubakar Shekau ya fitar na karshe, HumAngle ta ce ya dauko bayanin Boko Haram da kungiyar Al-Qaeda da ISIS.
Jaridar ta bayyana cewa Abubakar ya yi wannan bayani wanda ba kasafai aka saba jin sa ba. A wannan sako da shugaban Boko Haram ya fitar daf da zai mutu, ya bayyana abubuwan da suka jawo sabani tsakaninsu da kishiyar kungiyar ISWAP.
Shekau ya yi wannan magana ne a gaban wata tawaga, inda ya fadi salsalar alakarsa da Al-Qaeda da mubaya’ar da suka yi wa ISIS. “Asali, lokacin da muka fara shigowa jeji da zama, ku saurari bayani na da kyau… da farko na yi mubaya’a ga kungiyar Al-Qaeda.” Inji Abubakar Shekau.
Daga nan sai tsohon shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga cewa akwai wani yaron ‘yan ta’addan da ke raba masu kayan yaki a Najeriya da Mali. Bayan wata tafiya da aka yi, wannan mutum ya dawo masu da Naira miliyan 50 da makamai.
Da yake wannan jawabi, Shekau bai yi cikakken bayani a game da wannan kudi ba, amma ya ce wadannan miliyoyi sun jawo baraka a tafiyar Boko Haram.
Wasu daga cikin sojojin Boko Haram, a cewar Shekau, sun bukaci ya raba masu wannan kudi domin su yi amfani da shi, da alama bai yarda da hakan ba.
Daga baya hukuma ta yi ram da wannan mutumi da ke taimaka wa ‘yan ta’addan, aka daure shin a watanni shida yayin da yake kokarin kai sako daga kasar Mali.
Shekau ya bada labarin yadda aka bashi shawarar ya yi wa shugaban ISIS mubaya’a, Abu Bakr al-Baghdadi, hakan ya sa aka tabbatar da shi a matsayin gwamna.