Jagoran ‘yan uwa musulmi wadanda aka fi sani da ‘yan shi’a Sheikh Ibrahim Zakzaky ya rabbaba kayan abinci a watan azumi ga mabukata da makota.
A wani rahoto da kafar sadarwa ta ABS CHANNEL ta rawaito ya bayyana cewa shehin malamin ya saba wannan aikin alheri duk shekara idan watan ibada na ramadana ya zagayo
Rahoton ya bayyana cewa Sheikh Zakzaky ya saba wannan rabon kayan abinci shekaru masu yawa da suka gabata tun yana unguwar kwarbai a birnin Zariya kafin daga bisani ya koma unguwar Gyallesu duk a birnin Zariya.
Rahoton ya bayyana cewa kisan kiyashin Zariya wanda ya gudana a lokacin gwamnatin Shugaba Buhari bai hana shehin malamin cigaba da wannan aikin jinkai ba, domin har zuwa lokacin hada wannan rahoton Malam Zakzaky bai gushe ba duk shekara ya kan raba kayan abincin ga masu bukata.
Kane kuma shakiki ga Malam Zakzaky, Malam Badamsi Yaqoob ne ya jagoranci rabon kayan abincin kuma a takaitaccen jawabin sa da wakilan ABS CHANNEL Malam Badamasi ya bayyana cewa wannan wani aiki ne wanda dan uwan nasa ya saba gabatarwa duk shekara kuma a ranar 7 ga ramadan wadannan kaya sun iso kuma an raba su ga dinbin jama’a kama daga wadanda sunan ke a rubuce dama wadanda ba’a rubuta sunayen su ba tun fari.
Malam Badamsi ya bayyana cewa, sakamakon yanayi da mutane suka shiga tun rajab suke samun mutane masu bukatar a sanya su cikin wadanda za’a taimakawa a wannan shiri.
A karshen jawabin sa Malam Badamasi yayi addu’ar lafiya gami da nasara ga yayan sa Sheikh Ibrahim Yaqoob Zakzaky.
Itama a bangaren ta ‘yar uwa ga Sheikh Zakzaky, Malama Maimuna ta bayyana yadda mutane ke jin dadin wannan tallafi har wasu kan fashe da kuka saboda jin dadi.
Sheikh Zakzaky wanda ke zaman jiran takardun sa na tafiya domin fita kasashen ketare neman lafiya wacce ya rasa tun bayan kisa kiyashin zariya na shekrar 2015, a baya bayan nan rahotanni sun tabbatar da cewa, kotu a babban birnin tarayyar Abuja ta kori karar da ya shigar domin sanya kotu ta tursasa hukumomi masu ruwa da tsaki su saki fasfon sa dana mai dakin sa Malama Zinatuddin.