Sanata Shehu sani yayi Allah wadarai kan bayanin da wani malamin Izala yayi a kan matar shugaban kasa Olaremi Tinubu.
Kamar yadda Legit ng suka rawaito, Shehu sani yace malamin izalar yayi kira da a kashe sanata Olaremi wanda hakan ya wajabta ayi Allah wadarai da zancen malamin izalar.
Yayin da ‘yan Najeriya masu amfani da kafafen yada labarai suka tashi mai da martani sunyi kira ga Shugaba Tinubu da ya kama malamin ba tare da bata lokaci ba.
Sanata Shehu sani ya bayyana rashin yarda da batun bayan da malamin izalar ya bayyana cewa Olaremi ta cancanci a kashe ta saboda zaman ta fasto.
Shehu sani ya soki malamin inda yace sukar gwamnati ‘yancin kowanne Dan Kasa ne amma kiran a kashe matar shugaban kasa sam ba karbabben abu bane.
A wani bidiyo da aka yada a kafar sadarwa ta X ya nuno malamin yana cewa tikitin muslim muslim wanda ya kawo Tinubu kan mulki damfara ce kawai.
Sahara Reporters ta tabbatar da cewa malamin wanda har zuwa lokacin da Legit ng take tattaro wannan rahoto bata tabbatar wanene ba yace zaman Olaremi kafira ya zama wajibi a kashe ta, kamar yadda yace Qur’ani ya tabbatar.
Amma bai kawo ayar Alqur’ani tana goyi bayan ikirarin sa ba.
Diyar Shugaban Kasa Ta Bukaci Ayi Hakuri Da Mahaifin Ta
A wani labarin na daban diyar tinubu ta roki ‘yan Najeriya suyi hakuri da mahaifin ta a dai dai lokacin da ake fama da matsin tattalin arziki.
Folashade Fola- Ojo, kamar yadda Legit ng ta rawaito ta bayyana cewa mahaifin ta yana nufi alheri ne ga Najeriya kuma lokaci zai tabbatar da hakan.
Duba Nan: Zulum Ya Bude Kasuwar Banki Da Rikicin Boko Haram Yayi Dalilin Rufewa
Diyar shugaban kasan tayi wannan bayanin ne awanni bayan dan uwan ta seyi ta tabbatar da cewa Najeriya tana amintaccen hannu a hannun Shugaba Tinubu.