Shehu Sani ya shiga maganar zargin da ake yi wa Kashim Shettima na alaka da ‘Yan Boko Haram.
Tsohon ‘Dan Majalisar ya bayyana cewa tsohon Gwamnan na Borno bai da alaka da ‘Yan ta’adda Bugu da kari, Sanata Shehu Sani ya bayyana irin kokarin da Gwamnatin Shettima ta yi a Borno.
Legit.ng ta ce Shehu Sani wanda ya yi kaurin suna a fafutuka da gwagwarmaya, ya tofa albarkacin bakinsa game da takarar shugaban kasa.
Sanata Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar dattawa ya soki zargin da ake yi wa Sanata Kashim Shettima na alaka da ‘Yan Boko Haram.
Da yake magana a wani jawabi da ya fitar a ranar Litinin, 11 ga watan Yuli 2022, Shehu Sani ya nuna ba daidai ba ne a jefi Shettima da wannan mugun zargi.
Sanatan yake cewa babu laifi idan wasu sun nuna fushinsu a game da yadda APC ta yi watsi da Kiristoci, ta tsaida Musulmi da Musulmi a babban zaben Najeriya.
Babu adalci a zargin da ake yi Amma ‘dan siyasar yana ganin wuce gona da iri ne a jefi Kashim Shettima da wata alaka da ‘Yan ta’addan da ya taimaka sosai wajen ganin bayansu a Borno.
Sanata Shettima shi ne Gwamna a lokacin da rikicin Boko Haram ya yi kamari a Arewa maso gabas, yanzu ya zama ‘dan takarar mataimakin shugaban kasa.
“Shettima da yake Gwamnan Borno ya batar da lokacinsa, karfinsa da dukiyar jihar Borno sosai wajen yaki da fito-na-fito da magance matsalar ‘yan ta’addan.”
“Shettima bai da hannu wajen dauke ‘Yan matan Chibok. Ya fi kowa kokari wajen taimakawa aikin sojoji da jami’an tsaro wajen kare Borno da kasa.”
Shehu Sani Sani yake cewa a matsayin mai ruwa da tsaki, kuma tsohon shugaban kwamiti majalisar dattawa a kan rikicin Arewa maso gabas, ya san irin kokarin Shettima.
A rahoton This Day, an ji tsohon ‘dan majalisar yana mai cewa Shettima ya kawo kungiyoyi masu zaman kansu watau NGOs da kasashe domin su taimakawa yankin.
Shettima ya cancanta:
Shehu Sani Duk da shi ba ‘Dan APC ba ne kamar yadda ya fada, Shehu Sani ya ce maganar gaskiya Shettima ya fi sauran wadanda ake tunanin za a ba tikitin cancanta.
Mutane ba su dauki addini da wasa a Najeriya ba, amma duk da haka, tsohon Sanatan yana ganin Najeriya za ta amfana da kwarewar Shettima a harkar tsaro.
Tony Princewill ya bar APC A jiya an labari Tony Princewill ya yi fushi da Bola Tinubu ya yi fatali kiristocin da ke Arewacin Najeriya, ya dauko Musulmi a matsayin abokin takararsa a zaben 2023.
Source:hausalegitng