Senegal ta fara zaman makokin mutuwar ‘yan kasar a hadarin mota
A wannan Litinin din ne al’ummar Senegal ke fara zaman makokin kwanaki uku a faɗin ƙasar don juyayin waɗanda suka mutu a wani haɗarin mota mafi muni a tarihin ƙasar.
Lamarin ya faru ne a kusa da birnin Kaaffrine, bayan wasu motocin safa biyu sun yi taho mu gama da juna.
Shugaba Macky Sall ya ce gwamnatin ƙasar za ta yi zaman gaggawa a wannan Litinin din domin ɗaukar matakan kariya da suka dace.
Hatsarin ya kasance ɗaya daga cikin munanan hatsarin mota da ƙasar ta taɓa fuskanta a shekarun baya-bayan nan.
Haka kuma a wata mai kama da wannan aƙalla mutum 21 ne suka mutu a lokacin da wata motar bas da ke kan hanyarta ta zuwa birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta faɗi jim-kaɗan bayan da ta tsallaka kan iyakar Uganda da Kenya.
Jami’an yan sanda su ce tsananin gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin.
‘Yan sandan Uganda sun ce an samu fiye da haɗura 100 a cikin kwanaki uku a ƙasar cikin sabuwar shekara, lamarin da a cewarsu ya yi sanadin mutuwar mutum 35.
Read More :
‘Zan iya sayar da gidana don biyan ƴan fashi su sako min ƴata’.
Sabon rikici ya kunno kai a jam’iyyar PDP reshen Kano.
Shugaban Masu Rinjaye Na Majalisar Dokokin Jihar Kwara, Magaji, Ya Kwanta Dama.