Senegal ta ayyana makokin kwana uku bayan mutum 40 sun mutu a hatsarin mota
Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall ya ayyana hutun kwana uku a ƙasar domin yin makokin mutum 40 da suka mutu bayan wani mummunan hatsarin mota a ƙasar.
Hatsarin wanda ya rutsa da manyan motocin ɗaukar fasinja biyu – waɗanda suka yi taho mu gama da asubahin ranar Lahadi – ya yi sanadin mutuwar mutum 40 tare da jikkata wasu gommai.
Shugaba Mucky Sall ya ce gwamnatin ƙasar za ta yi zaman gaggawa ranar Litinin domin ɗaukar matakan kariya da suka dace, bayan hatsarin wanda ya kasance ɗaya daga cikin munanan hatsarin mota da ƙasar ta taɓa fuskanta a shekarun baya-bayan nan.
Haka kuma a wata mai kama da wannan aƙalla mutum 21 ne suka mutu a lokacin da wata motar bas da ke kan hanyarta ta zuwa birnin Nairobi na ƙasar Kenya ta faɗi jim-kaɗan bayan da ta tsallaka kan iyakar Uganda da Kenya.
Jami’an yan sanda su ce tsananin gudun wuce kima ne ya haddasa hatsarin.
‘Yan sandan Uganda sun ce an samu fiye da haɗura 100 a cikin kwanaki uku a ƙasar cikin sabuwar shekara, lamarin da a cewarsu ya yi sanadin mutuwar mutum 35.