Yanzu dai saura kwanaki 20 wa’adin damar daukaka karar da kotun ta baiwa Malam Abduljabbar.
Gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta fara aiwatar da umurnin da kotun shari’a ta yiwa Abduljabbar.
Kotun a kimanin makonni biyu da suka gabata ta yankewa Abduljabbar hukuncin kisa ta hanyar rataya.
Gwamnatin jihar Kano ta fara aiwatar da umurnin da Alkalin kotun shari’a, Ibrahim Sarki-Yola yayi kan Sheikh Abduljabbar Nasiru-Kabara.
Legit Hausa ta ruwaito muku hukuncin da Ibrahim Sarki-Yola ya yanke kan AbdulJabbar ranar 15 ga watan Disamba bayan kama shi da laifin batanci ga Manzon-Allah (SAW) a wa’azozinsa.
Bayan hukuncin kisa da aka yanke masa, Alkalin ya bada umurnin rufe Masallatansa, makarantarsa, kuma a daina sanya karatukansa a gidajen rediyo da talabijin.
Hakazalika ya umurci kwashe littafansa guda 189 kuma a gurfanar gaban kotu.
Masallatan sun hada da na Filin Mushe da Sharada
Daily Nigerian ta ruwaito cewa a ranar Juma’a, gwamnatin jihar ta aiwatar da da wadannan umurni.
An tattaro cewa tuni an rufe Masallatan Malam AbdulJabbar biyu kuma jami’an tsaro sun mamaye wajen.
Hakazalika, an kwashe takardunsa 189 kuma an mayar da su dakin ajiya littafan gwamnatin jihar.
A wani labarin na daban yayin da Kiristocin Jihar Gombe ke bin sahun takwarorinsu na duniya wajen gudanar da bukukuwan Kirsimeti na bana, Gwamna Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bukace su da dabbaka dabi’un kauna, sadaukarwa da kuma hakuri kamar yadda koyarwa Yesu Almasihu ya horar da su.
A sakonsa na taya murna dauke da sanya hannun Ismaila Uba Misilli, babban daraktan yada labara gwamnan, ya bukaci mabiya addinin Kirista a jihar da ma daukacin al’ummar Nijeriya baki daya da su ci gaba da karfafa imaninsu da Allah, tare da tabbatar da zaman lafiya da hadin kai.
Ya kuma bukaci jama’a su sake sadaukar da kan su ga addu’o’i, abin da ya ce yana da matukar tasiri ga zaman lafiya da hadin kan al’umma.
Gwamnan ya bayyana cewa “A wannan muhimmin biki na Kirsimeti, ina mika sakon fatan alheri ga al’ummar Kirista da daukacin al’ummar kasar nan.
“Wannan lokacin yana tunatar da mu bukatar dabbaka kyawawan halaye na kauna, sadaukarwa da kuma hakuri.
Source:LegitHausa