Ya ce a halin yanzu akwai kasashen da gwamnatin Saudiyya ta sanar da cewa ‘yan wadannan kasashen ba za su iya zuwa kasar Saudiiya ba saboda dalilai na kiwon lafiya.
Ya ce wadanda suke bukatar zuwa aikin umrah daga wadannan kasashen, za su iya neman izinin shiga cikin kasar Saudiyya, daga kasashen da aka yarje musu shiga cikin kasar.
Ya ce hakan ya hada da neman visa da kuma tabbatar da cewa an samu rigakafin cutar corona na’in rigakafin da gwamnatin Saudiyya ta amince da shi a hukumance kafin shiga kasar.
Baya ga haka kuma, daga cikin sharuddan shi ne dole ne duk wanda ya shiga kasar, a duk lokacin da ya yi aikin ibada na Umrah, bayar ziyartar dakin Ka’abah da sa’io 6, dole ne ya kai kansa wajen jami’an kiwon lafiya, domin bincikar lafiyarsa.
A wani labarin na daban batun bude ofishin jakadanci da UAE ta yi a yau a Isra’ila, yana ci gaba da fuskantar kakkausan martani daga bangarori daban-daban na al’ummar falastinu, da kuma al’ummomin larabawa daga kasashe daban-daban, wadanda suke bayyana hakan a matsayin cin amanar Falastinawa da kuma al’ummar musulmi.
A cikin bayanin da ta fitar a yau kan wannan batu, kungiyar Hamas ta mayar da kakkausan martani a kan gwamnatin kasar Hadaddiyar Daular Larabawa, inda ta bayyana hakan a matsayin babban zunubi da kuma cin amanar al’umma.
Hamas ta ce, abu mafi muni dangane da wannan mataki na Hadaddiyar Daular Larabawa shi ne, hakan yana zuwa ne ‘yan kwanakin bayan kisan kiyashin da Isra’ila ta yi a kan Falastinawa a yankin Zirin Gaza, tare da kashe mata da kananan yara, maimakon daukar matakin ladabtarwa a kan Isra’ila, sai aka dauki matakin kara kulla dankon alaka da kauna a tsakaninsu.
Kafofin yada labaran Isra’ila sun bayar da rahoton cewa, a yau ne aka gudanar da bikin bude bude ofishin jakadanci na kasar Hadaddiyar Daular Larabawa wato UAE, a birnin Tel Aviv fadar mulkin gwamnatin yahudawan Sahyuniya.
Taron ya samu halartar manyan jami’an gwamnatin yahudawa, da suka hada da shugaban Isra’ila Ishaq Herzog, da kuma ministan harkokin wajen gwamnatin yahudawan Yair Lapid, gami da wasu daga cikin manyan jami’an Isr’ila, da kuma jami’an gwamnatin hadaddiyar daular larabawa, da kuma wasu jami’an gwamnatocin larabawa masu alaka da Isra’ila.