Saudiyya ta buƙaci limamai su daina tsauwalawa a addu’ar Al-ƙunutu na sallolin tahajjud.
Ma’aikatar Harkokin Addini ta Saudiyya ta jaddada wa limamai a masallatan ƙasar da ke jan sallar dare ta tahajjud da su daina tsawaita addu’o’in Al-ƙunutu don sauƙaƙa wa masallata, a cewar rahoton saudi Gazette.
Rahoton ya ce an nemi limaman su kammala sallar da wuri kafin kiran sallar asuba don mutane su samu isasshen lokaci tsakanin sallolin biyu.
Musulmai na yin sallar tahajjud ne da tsakar dare a kwana 10 na ƙarshen watan Ramadana. A yau Asabar ake cika kwana na 15 da fara azumin na Ramadana, wanda Musulamai za su shafe kwana 29 ko 30 suna yi.
Kazalika, ma’aikatar ta umarci dukkan masallatai su yi aiki da koyarwar Annabi Muhammadu S.A.W. game da addu’ar da aka ruwaito yana yi yayin addu’ar Ƙunutu.
READ MORE : Kungiyar Hamas Ta yi Kira Ga Falasdinawa Da Su Yi Gangami A Masallacin Quds A Gobe Juma’a.
“Ma’aikatar ta nemi limamai su guji tsawaita addu’o’i har ma su mayar da su matsayin huɗuba. Kuma ya kamata su guji zuzuta murya da kuma yin ƙafiya, ana so su yi addu’a cikin ƙanƙan-da-kai da kuma tawalu’u,” in ji rahoton.
READ MORE : Yin Murabus Din Buhari Ba shi Ne Mafita Ga Matsalolin Tsaro Da Kasar Ke Fuskanta Ba.