Sau biyar ina yunkurin sasantawa da Wike – Atiku
Dan takarar shugabancin Najeriya a jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya ce sau biyar yana yunkurin yin sulhu kan rikicin jam’iyarsu da gwamnan jihar Ribas Nyesom amma hakan ya ci tura.
Atiku Abubakar ya ce yanzu yana jiran bangaren su Wike ne don ganin sun kawo karshen rikicin da jam’iyyar tasu ke fama da shi.
Atiku Abubakar ya bayyana hakan ne a yayin taron tattaunawa da ‘yan takarar shugabancin Najeriya da gidan talabijin din Channels, ya gabatar a ranar Lahadin karshen makon da ya gabata.
Atiku Abubakar ya ce “na same shi a Abuja sau biyu, na kuma same shi a Patakwal sau biyu, sannan kuma a Landan sau daya.”
Sai dai Atiku bai yi wani karin bayani ba dangane batutuwan da suka tattauna da Wike a ganawar da ya ce sun yi ba.
Ya ce yana zargin kansa kan yadda suka gaza shawo kan rikicin.
Sannan ya ce matsalar daga bangaren Wike take ba daga gare shi ba.
Takaddamar da jam’iyyar PDP ke fama da ita, ta soma asali ne tun bayan da Atiku abubakar ya zaɓi Ifeanyi Okowa , a matsayin mataimakinsa, bayan zaɓen fitar da gwani na jam’iyyar ta PDP da ake gudanar a ranar Asabar 28 ga watan Mayun 2022.