Fadar mai Alfarma Sarkin Musulmai ta bukaci a fara duban jinjirin watan Sha’aban 1444 AH daga ranar Litinin.
A wata sanarwa da Sultan ya fitar ranar Lahadi, ya ce ranar Litinin ta kama 29 ga watan Rajab, 1444 AH daidai da 19 ga watan Fabrairu, 2023.
Daga watan Sha’aban sai watan Ramadana wanda Musulmai ke azumtar shi baki ɗaya kamar yadda Addini ya wajabta masu.
Mai Alfarma Sarkin Musulmi kuma shugaban majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci a Najeriya, Alhaji Sa’ad Abubakar III (Sultan na Sakkwato) ya fitar da sabuwar sanarwa.
Sultan ya umarci ɗaukacin al’ummar Musulmai a Najeriiya su fara duba jinjirin watan Sha’aban 1444 AH daga ranar Litinin 29 ga watan Rajab, 1444 daidai da 20 ga watan Fabrairu, 2023.
Ramadan Ya Matso: Sarkin Musulmi Ya Umarci
A Fara Duba Jinjirin Watan Sha’aban Hoto: Sultan Asali: Twitter Sarkin Musulmin ya ba da wannan umarni ranar Lahadi a Sakkwato a wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun Farfesa Sambo Junaidu, shugaban kwamitin harkokin addini na fadar Sultan Sakkwato.
Jaridar Daily Trust ta rahoton Sanarwan na cewa: “Muna sanar da ɗaukacin al’ummar Musulmai cewa ranar Litinin 29 ga watan Rajab, 1444 AH wacce ta yi daidai da 20 ga watan Fabrairu, 2023, ita ce ranar da ya kamata a fara duba jinjirin watan Sha’aban, 1444 AH.”
“Saboda haka muna buƙatar Musulmai su fara duba jinjirin watan Sha’aban daga ranar Litinin kuma su kai rahoto ga Hakimi ko Dagacin gari mafi kusa idan sun ga watan domin sanar da Sultan.”
Bayan haka Sultan ya roki Allah SWT ya shiga lamarin Musulmai ya basu karfin ikon sauke hakkoki da nauyin da addini ya ɗora masu, Ameen, kamar yadda PM News ta rauwaito.
Watan Sha’aban shi ne wata na 8 a cikin jerin watannin Kalandar Musulunci kuma shi ne watan da Ramadan ke biye masa.
A watan Ramadan ne Allah ya shar’anta wa Musulmi Azumi tun daga farko har ƙarshe kuma watan na da dumbin falala sannan daren Lailatun kadari na zuwa a cikin watan na Azumi.
Sauya Naira: Mutane Suna Cikin Yunwa Kuma Sun Fusata, Sultan
A wani labarin kuma Sarkin Musulmai a Najeriya ya yi magana kan halin da ake ciki sakamakon sauya fasalin naira da CBN ya yi Alhaji Sa’ad Abubakar III ya ce mutane sun shiga halin ƙunci da kuma yunwa kuma basu samun sabbin kuɗin domin gudanar da rayuwarsu ta yau da kullum.
Basaraken ya faɗa wa gwamnati da sauran masu alhaki a kan lamarin mafita ɗaya kafin wahala ta kai yan Najeriya bango.
Source:LegitHausa